Majalisar wakilai ta bukaci Babban Bankin Nijeriya (CBN), da ya dakatar da aiwatar da sabon tsarin kayyade kudaden da aka shirya gudanarwa a ranar 9 ga watan Janairu, 2023, har sai an cika sharuddan dokar da ta kafa bankin koli.
Majalisar ta kuma gayyaci gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emiefele, bisa tanadin dokar babban bankin, domin ya yi wa majalisar bayanin manufofin tsarin da CBN ya fito da shi.
- An Wallafa Bayanin Xi Jinping A Jaridar Saudiyya
- An Maka TikTok A Kotu Kan Nuna Wa Yara Bidiyoyin Badala
Mambobin majalisar wakilai ta kasa, wadanda suka bi diddigin sun yi Allah-wadai da sabuwar manufar cire kudaden, sun yi hasashen cewa hakan zai yi matukar shafar kananan ‘yan kasuwa da tattalin arziki tunda galibin al’ummomin karkara ba su da damar amfani da banki.
Majalisar, ta umarci gwamnan CBN da ya gurfana a gabanta a ranar Alhamis 15 ga watan Disamba, 2022, domin yi wa ‘yan majalisar bayani kan dalilin da ya sa aka kirkiri manufar takaita fitar da kudaden.
Tun da farko CBN ya fitar da dokar cewar Naira 20,000 kacal mutum zai iya cirewa a rana, sai dubu 100,000 a cikin wata guda.