Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya bukaci yan siyasa a jihar Yobe su guji kalaman da za su jawo tada zaune tsaye a lokutan yakin neman zaben da yake gudana a fadin kasar nan; musamman a jihar Yobe.
Gwamnan ya bayyana hakan ta bakin Babban Mai Taimaka masa ta kafafin sadarwa na zamani, Mallam Yusuf Ali, inda ya ce a matsayin Gwamna Buni ma’abucin son zaman lafiya da sasanci, wanda hakan ya sanya ake masa lakabi da ‘Limamin-sulhu’, ya bukaci yan siyasa su zauna lafiya a lokacin da suke gudanar da yakin neman zaben mai zuwa na 2023.
Yusuf Ali ya kara da cewa, “Hon. Mai Mala Buni mutum ne mai matukar kaunar wanzuwar zaman lafiya da yaduwar fahimtar juna daga kowane bangaren al’ummar (yan siyasa).
Musamman a daidai lokacin da ake tunkarar zaben 2023, wanda abubuwan da za su sa a samu nasarar gudanar da zaben shi ne zaman lafiya. Yada maganganun gaba ko kiyayya a tsakanin al’umma ba zai haifar mana da-mai-ido ba, domin ko shakka babu dukkanin mu ‘ya’yan jihar Yobe ne, babu dalilin da zai sa mu rura wutar gaba ko kyama a tsakaninmu.”
Mallam Yusuf ya kara da cewa, kowane lokaci Gwmnan ya kan nanata muhimmancin zaman lafiya da fahimtar juna, wanda ko a kwanan baya, a sa’ilin da yake kaddamar da kasafin kudin wannan shekara a gaban Majalisar Dokokin jihar Yobe ya jadda batun ‘yan siyasa’ su guji kalaman da zasu kawo tashin-tashina ko kiyayya da makamantan su.
Gwamna ya ce, “Ina so na tunatar da mu cewa, a yayin da muke tunkarar babban zaben 2023, ya dace ace dokokin zabe na kasa su ne za su ci gaba da yi mana jagoranci, tare da kokari wajen abubuwan da za su kawo ma na hadin kai da zaman lafiya, tare da yin watsi da kalaman kiyayya ko tunzura jama’a.
Sannan mu na iya kasancewa ma su bambancin ra’ayin siyasa, amma wannan ba zai sanya mu kasance makiyan juna ba. A matsayinmu na ‘yan jihar Yobe, bai dace ace mun jefa kanmu a cikin tashin hankali da juna ba, domin wata bukatar son zuciyarka.”Gwamna Buni ya ce, “ina tabbatar muku da cewa, wannan gwamnati za ta ci gaba da aiki don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa da ci gaban wannan jihar da na al’ummarmu baki daya.
Don haka, ina rokon ku, ku ci gaba da yin addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya da ci gaban jihar Yobe da ma kasarmu Nijeriya baki daya.”