A yau mun kawo ra’ayoyinku ne a kan wa’adin zuwa ranar 31 ga watan Disamba da Shugaba Buhari ya ba jami’an tsaron na su kawo karshen ayyukan ta’addanci a Nijeriya. Shin akwai yiwuwar cimma wannan wa’adin kuwa? Ga bayanan da mas bibiyar ska yi
Comr Isma’il Ibrahim Gusau
Wannan labarin mun saba jinshi ga bakin shugaban kasa da manyan masu ruwa da tsaki a kan sha’anin tsaro, ba’a biyo hanyar magance matsalar tsaro ba a Nijeriya, tayaya za a ce dan ta’adda yafi gwamnati mallakar makamai kaga harkar tsaron kasar nan akwai lauje cikin nadi.
Kuma idan ka duba ko yaushe magana daya ce suke yi wa ‘yan kasa babu wani sauyi da ake samu itace tun yana danye ake lankwasa shi, amma yanzu kam sunyi sake, duk abinda baka gyara ba shekara bakwai da rabi yanzu wane gyara akeso ayi. Allah dai ya zaba muna shugabanni nagari.
Muhd Basheer Sa’ad
An dade ana ruwa kasa tana shanyewa! Kawo yanzun dai mun san wannan magana ta Shugaban Buhari kanzon kurege ce.
Domin kuwa a baya ya fadi hakan kuma babu abunda ya sauya. Abunda ya kamata kawai mu mika al’amuran mu ga Ubangiji kawai domin shi ne zai yi mana maganin su.
Abubakar Mohammed Joda
Muna fatan alkhairi a kullum ga jami’an tsaronmu, muna kuma addu’ar Allah ya kawo mana karshen ta’addanci a yankunanmu. Amma dai karya da farfagandar gwamnatin nan babu wanda bai ganeshi ba izuwa yanzu.
Real Miftahu Ahmad Panda
Ni dai ina ganin, abu ne mawuyaci hakan ya iya yiwuwa (ma’ana a iya kawo karshen ayyukan ta’addanci, a cikin wannan wa’adi), duba da yadda a baya ma, shugaban ya sha bada irin wannan umarni ga hafoshin tsaron kasar nan, amma shiru ka ke ji. Sai dai kuma, ba ma ce mun yanke kauna baki daya da yiwuwar hakan ba.
Fatan mu dai, Allah ya kawo mana karshen wadannan matsalolin tsaro da su ka ta’azzara, musamman ma a yankin Arewacin Nijeriya.
Amb Ibrahim Adam Dan-Sarauta
Ai ko wanda ba dan Nijeriya ba idan ya samu wannan labari ya san cewa abu ne da ba zai yiwu ba.
Balle mu da ke rayuwa cikin kasar kuma yankunan da ta’addancin ya ke faruwa.
Maganar Gaskiya ko da Buharin da kansa zai fito ya yi aikin tare da Jami’an tsaro ina mai tabbatar miki da cewa ba za a iya kawo karshen abin a wa’adin da aka diba ba.
Abin da ya fi dacewa da mu shi ne Addu’a. Allah ya kawo mana karshen wannan ta’addanci ya ba mu shuwagabanni na gari. Wanda za su nuna jin zafin abin ta yadda za a magance matsalar.
Khadija Muhammad
Da ikon Allah mu kasance masu fatan nasara ba màganganun banza ba
Mohammed Inuwa
Wannan mataki da Shugaban Kasa ya dauka ya yi daidai. Domin kadan akwi kayan aiki da hakan zai yiwu InshaaAllah. Kuma muna addu’a da kara bawa gwamnati hadin kai. Allah kawo kasarmu zaman lafiya.
Comr Hassan S Umar
Idan kin san abinda ake cewa shifcin Gizo! To wannan shi ne Shifcin Gizo, magance matsalar tsaro yana daya daga cikin 3 majors na abubuwan da suka kafa gwamnatin Buhari A 2015 saboda tsananin takura da harin ‘yan ta’adda a Nijeriya musamman Arewa. Amma gashi yau shekara kusan 8, an kusa kamala wa’adi na biyu amma.
Kar ku manta a wannan gwamnatin aka samu kungiyar ikirarin jihadi ta (ISWAP) a yankin arewa maso gabas.
Kar ku manta a wannan gwamnatin aka samu harkokin garkuwa da mutane a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, haka kuma a wannan lokacin ne aka samu ayyukan ‘yan tawayenh Biyafra ya kara karuwa. Muna dai rokon Allah ya taimaka wa jami’antsraomu donj su samju nasarar da ake bukata a kan ayyukan ‘yanta’adda a sassan Nijeriya
Sulaiman Muhammad
Gaskiya mai girma shugaban kasa yasha fadin haka saboda babu wani abu da zai canza.
Domin matsalar tsaron Nijeriya akwai Turawan yamma da Amurka da ‘yan Nijeria da masu mulkin Nijeria duk sun san komai basu yi niyar gyaran ba ne
Widad Isma’il
Allah ya basu ikon aiwatar da abinda zamu yi masu shi ne addua, amma gaskiya al’amarin tsaro abin dubawa ne tunda har za a iya kamo wanda suke cin zarafin manya a hukuntasu, a ganina kamo wadanda suke ta’addanci binciko su abu me sauki, inda gaske ake yi.