Alkalin babbar kotun tarayya A.M. Liman, ya sanya ranar 19 ga watan Janairu, 2023 a matsayin ranar yanke hukunci kan cewa Muhammad Sadiq Wali ba ya a cikin rikicin da ke ake ci gaba da yi da shi da Muhammad Sani Abacha, a kan zaben fidda gwani na takarar gwamna a jam’iyyar PDP a Jihar Kano.
Tun da farko, kotun ta tarayyar ta sanya ranar 8 ga watan Disamba 2022, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a kan zaben fidda gwani na PDP guda biyu tsakanin Abacha da Wali wanda dukkaninsu, ke ikirarin sun lashe zaben.
- Shugaban Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Da Manyan Shugabannin Kasar Saudiyya Da Kuma Gana Da Shugabannin Wasu Kasashen Larabawa Bi da Bi
- Yadda Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ke Bunkasa Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa
Alkalin kotun ya sanar da cewa akwai karin wata takarda da lauya mai tsaya wa Wali, ya gabatar wa da kotun, amma lauyan da ke tsaya wa Abacha ya karyata wata masaniya game da takardar.
Liman ya ci gaba da cewa, takardar ta ce, a wani hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ta ce, kotun ta tarayyar, ba ta hurumin sauraren maganar saboda kotun ta daukaka karar ta yanke hukuncin cewa, a cire sunan Wali daga cikin karar da aka gabatar wa da kotun ta tarayyar domin bai da wata basaba da karar.
Amma lauya mai tsaya wa Abacha, Barista Reuben Atabor, ya shaida wa kotun cewa, hukuncin da kotun ta daukaka karar ba kotun tarayyar ce ta yanke shi ba.
Biyo bayan takadama a tsakanin lauya mai tsaya wa Abacha da lauya mai tsaya wa Wali, mai shari’a alkali Liman, ya dage yanke hukuncin saboda maganar takardar, inda ya warw ranar 19 ga watan Janairu 2023, don yanke hukunci kan hukuncin da kotun ta daukaka kara ta yanke.