Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa bisa jagorancin shugabanta, CGI Isah Jere Idris, ta ƙara matsa ƙaimin tabbatar da ingancin aikin da take yi wa al’umma a cibiyoyin mu’amalolinta da ‘yan ƙasa.
A sakamakon wannan sabon yunƙurin, shugabanta Isah Jere ya ƙaddamar da sabon katafaren ginin sashen kula da ingancin aiki da ake wa laƙabi da “SERVCOM”.
Da yake jawabi a yayin bikin, Isah Jere ya sanar da sabbin abubuwan da suke ɓullo da shi domin tabbatar da ingancin aikin samar da fasfo da sauran sassan ayyuka na hukumar.
Ya ƙara da cewa, “An samar da Sashen SERƁICOM na Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya don ingancin aiki mai alfanu don tabbatar da gamsuwar abokan ciniki da kuma cike giɓin da za a iya samu a tsakanin NIS da abokan hulɗarta wajen gudanar da aiki.
“Gabaɗaya dai, Serɓicom a matsayin sashe tana aiki ne bisa muradin Fadar Shugaban Kasa da Tsarin Sauƙaƙa Yin Kasuwanci, Inda NIS ta yi aiki kuma tana ci gaba da aiki sosai. Ya kasance a rubuce a tarihi cewa NIS ta zo na farko a kan tsarin sauƙaƙa Yin Kasuwanci na Shugaban Ƙasa har sau shida (bi-da-bi).
“Gwamnati aba ce da ta shafi jama’a kuma saboda jama’a, don haka, NIS ta mayar da hankali sosai a kan ingancin hidimar da ake yi wa ‘yan ƙasa da yadda ake biyan irin waɗannan buƙatu. Cibiyoyin gwamnati wakilci ne na gwamnati a matakai daban-daban. Galibi su ne tsarin ginshiƙan gwamnati, waɗanda ke zama wurin tuntuɓar jama’a da masu zaman kansu. A kan wannan NIS ba daban ba ce, ita ma tana ciki.
“Bari in tabbatar muku da cewa NIS ta himmatu wajen samar da sakamakon da ya dace da bukatun al’ummarmu ta yau ta amfani da kayan aikin da take da su a hannunta. Za mu kuma yi ƙoƙari mu yi wa duk masu ruwa da tsaki hidima cikin ƙayyadaddun lokuta mafi dacewa cikin ƙwarewarmu daidai gwargwado. Don haka muna kira ga jama’a da su ba mu goyon bayan da ya dace a ƙoƙarin da muke yi na bayar da gudunmawarmu ga samun ingantacciyar Nijeriya.” Ya bayyana.
Wakazalika, CGI Isah Jere ya hori jami’an hukumar manya da ƙananan kowa ya yi ƙoƙarin inganta ƙwarewar aiki, domin a cewarsa, babu wurin ɓuya ga raggwaye.
“Ina kira ga duk Jami’ai da su yi amfani da wannan damar don haɓaka ƙwarewar ayyukansu. Ina kuma iya sanar da dukkan Jami’anmu cewa daga yanzu, a yanzu babu wurin buya ga duk wanda yake wasa da gudanar da aiki mai inganci. Yarjejeniyar tsarin aiki da aka sake fasali, yunƙuri ne na hana ragwanci da gazawar aiki saboda ta bayar da cikakkun bayanai a kan yadda za a bi a riƙa mu’amalar aiki da hukumar, ko neman ƙarin bayani, ko gabatar da korafe-korafe da kuma yadda za a nemi gyara wani abu da aka tafka ba daidai ba.
“Ina so in yi amfani da wannan damar wajen sanar da jama’a cewa a wani bangare na kokarin tsaftace tsarin fasfo, Hukumarmu ta bullo da tsari wanda zai ba masu neman fasfo damar zabar ranar da za a dauki bayansu a cibiyoyin hukumar. Wannan zai taimaka wa masu aiki su daidaita tsarin fasfo yayin da kuma masu neman fasfo za su samu damar zaɓen ranar da suka ga ta fi kwanciyar musu a a kai.
“A madadin manya da ƙananan jami’an Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, ina jinjina wa gwamnati da al’ummar Jihar Filato bisa goyon bayan da suke bai wa ma’aikatanmu tsawon shekaru. Muna mika godiya ta musamman ga mai girma gwamna bisa goyon baya irin na uban ƙasa da yake bai wa Kwanturola na jihar da kuma sauran hidima da ake wa hukumar.” Kamar yadda ya bayyana.