• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Jarida Sun Karrama Mawallafin Blueprint, Mohammed Malagi

by Sulaiman
3 years ago
Malagi

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) ta ba Shugaban kamfanin buga jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, babbar kyautar karramawa ta ɗaya daga cikin manyan masu tallafa wa cigaban aikin jarida a ƙasar nan. A turance, sunan kyautar ‘Milestone Recognition Media Icons in Nigeria’.

An yi wa Malagi da wasu hamshaƙan ‘yan Nijeriya karramawar ne a wani gagarumin biki da aka yi ran Alhamis a Cibiyar MUSON da ke Legas.

  • Mohammed Idris Malagi A Ma’aunin Siyasa

Wasu waɗanda aka karrama sun haɗa da shugaban NUJ na ƙasa, Cif Chris Isiguzo, da Gwamnan Jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, da Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, Alhaji Usman AIkali Baba, da tsohon gwamnan Jihar Ogun, Cif Segun Osoba, da Ciyaman ɗin jaridun Vanguard, Mista Sam Amuka Pemu, da tsohon gwamnan Jihar Abiya kuma mamallakin jaridun Daily Sun, Sanata Orji Uzor Kalu, da Ciyaman na jaridun Thisday, Mista Nduka Obaigbena, da Ciyaman na kamfanin Daar Communication masu gidajen rediyo da talbijin na AIT da Raypower, Cif Raymond Dokpesi.

Wasu da su ma aka karrama su sun haɗa da Ciyaman na tashar talbijin ta Channels, Mista John Momoh, da tsohon babban editan mujallar The News, Mista Bayo Onanuga, da Ciyaman kuma jagoran kamfanin Media Trust masu jaridun Daily Trust da Aminiya, Malam Kabiru Yusuf, da Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Mista Buki Ponle, da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Alhaji Muhammad Garba, da Editan jaridar Champion na farko, Mista Emma Agu, da tsohuwar janar-manajar labarai ta gidajen rediyo da talbijin na AIT da Raypower, Madam Olufunke Fadugba, da Manajan-Daraktar jaridar The Point, Dakta Yemi Kolapo da mawallafin jaridar The Marketing Edge, Mista John Ajayi.

Malagi
Malagi (na 1 daga hagu) tare da wasu manya da aka karrama

Shugaban ƙungiyar ta NUJ, Cif Chris Isiguzo, ya yi bayanin cewa karramawar da aka yi wa Malagi an yi ta ne saboda ganin ya tsaya ƙyam da ƙafafun sa wajen ciyar da aikin jarida gaba a tsawon shekaru, wanda ya tabbatar da cewa shi da sauran waɗanda aka karrama ɗin sun yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da wanzuwar ‘yancin ‘yan jarida, wanda wani ginshiƙi ne na kafuwar mulkin dimokiraɗiyya a faɗin duniya.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja

An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

Ya ce yaƙin da waɗannan masu tallafa wa ‘yancin aikin jarida ke yi ya na taimakawa wajen habaka dimokiraɗiyyar ƙasar nan wajen tabbatar da gaskiya a gudanar da mulki, tsare gaskiya, bin doka da oda da kuma bai wa kowa damar ya shiga a dama da shi a fagen lamurran jama’a da kuma siyasa.

Isiguzo ya ƙara da cewa: “Ya na su samu walwala, ya wanzar da yanayin aiki tare da kuma zurfafa dimokiraɗiyya ta hanyar ba kowa da kowa dama a yanayi na ‘yanci, zaman lumana da samun cigaba a alƙiblar da ake so a fuskanta.

“Waɗannan mutanen da mu ke karramawa a yau sun nuna jajircewa ta wannan fuskar kuma mu na yaba masu saboda hakan. Ya kamata a lura da cewa muhimmancin ‘yancin aikin jarida a wajen gudanar da mulki mai nagarta da habaka dimokiraɗiyya da aikin gina ƙasa ba abin wasa ba ne.

“Sai dai kuma, duk da yake ana ganin alfanun aikin jarida, ‘yan jarida da dama a Nijeriya su na ci gaba da fuskantar tsangwama da barazana da lahanta masu jiki da ake yi a lokacin da su ke gudanar da aikin su na halaliyar su.

Malagi
Malagi (na 1 a dama) lokacin da Sam Amuka Pemu (l) ya ke gaisawa da Cif Segun Osoba

“Irin bajinta da sadaukarwar waɗannan ‘yan jarida ya sa mu ke karrama su a yau a karo na farko na karramawar ‘Milestone Recognition of Media Icons’. Don haka ne mu ke so mu riƙa yin wannan taron a kai a kai.

“An shirya wannan taro ne domin a karrama tare da nuna girmamawa ga wasu daga cikin waɗannan gwarzaye domin a ƙarfafa wa sauran ‘yan jarida gwiwa, sannan a ƙarfafa aikin jarida mai nagarta, da ‘yancin aikin jarida da kuma ingantaccen mulki a Nijeriya.”

Shugaban taron kuma tsohon gwamnan Jihar Ogun, Aremo Olusegun Osoba, ya yi kira ga ƙungiyar ta NUJ da ta tashi tsaye ta magance yawaitar kafafen yaɗa labarai na intanet da ake samu waɗanda ya ce su na bata sunan aikin.

Osoba ya yi kira ga NUJ da ta samar da wani gidan yana inda za ta yi wa dukkan ‘yan jaridar da ake aiki a Nijeriya rajista.

Alhaji Mohammed Idris Malagi, wato mawallafin Blueprint da Manhaja, wanda kuma shi ne Kakaaki Nupe, har ila yau ɗan siyasa ne a Jihar Neja inda ya yi takarar zama gwamna a jam’iyyar APC a zaɓen fidda gwani da aka yi a watannin baya.

Ya samu rakiya zuwa taron karramawar a Legas ta ‘yan’uwa da abokan arziki. Sun haɗa da tsohon mataimakin gwamnan Jihar Neja kuma tsohon Jakaden Nijeriya a Afrika ta Kudu, Alhaji Ahmed Musa Ibeto; da Shugaban APC na Jihar Neja, Honourable Haliru Zakari, da tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Honourable Ibrahim Ebbo.

Waɗansu ‘yan rakiyar sun haɗa da babban ɗan kasuwar nan mai harkar inshora, Alhaji Abdulmalik Abubakar Muye, da Babban Kwamishina a Hukumar Sauraren Ƙararrakin Jama’a, Barista Bala Marka, da wani wanda ya yi takarar zama gwamnan Neja a bana, Alhaji Aliyu Idris Rugga, da kuma Sakataren APC na Jihar Neja, Khaleel Ibrahim Aliyu.

Sauran su ne tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Magama ta Jihar Neja, Honourable AIhassan Ibeto, da Ma’ajin APC na jiha, Dakta Idris Mohammed Gbangba, da Shugaban Matasan APC na jiha, Comrade Abdullahi Suleiman, da zaɓabben Shugaban Ƙaramar Hukumar Lavun ta Jihar Neja, Honourable Isah Kutigi, da dattijo a APC kuma babban ɗan kasuwar nan, Honourable Theo Mamman, da Alhaji Umar Mohammed Wara da fitaccen ɗan APC a Jihar Neja, Honourable Ndagi Lavun.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: Wata Tankar Mai Ta Sake Fashewa A Neja
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja

October 21, 2025
An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba
Manyan Labarai

An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

October 21, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa
Ra'ayi Riga

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 21, 2025
Next Post
Malagi

Yadda Bikin Bai Wa Sarkin Kagara Sandar Girma Ya Gudana

LABARAI MASU NASABA

Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

October 21, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Wata Tankar Mai Ta Sake Fashewa A Neja

Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja

October 21, 2025
Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia

Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia

October 21, 2025
Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya

Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya

October 21, 2025
An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

October 21, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 21, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC

Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC

October 21, 2025
NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

October 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu

October 21, 2025
Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.