• Leadership Hausa
Sunday, June 4, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Bikin Bai Wa Sarkin Kagara Sandar Girma Ya Gudana

by Muhammad Awwal Umar
6 months ago
in Masarautu
0
Kagara
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya mika wa mai martaba Sarkin Kagara, Malam Ahmad Garba Gunna (Attahiru II) sandar girma a garin Kagara. Bikin rantsuwar kama aiki da karban sandar ya kasance ne a filin wasa na garin Kagara a ranar Asabar da ta gabata.

Tun da farko Alkalin-alkalan jihar, Mai Shari’a Halima Ibrahim Abdulmalik ta rantsar da sabon sarki. Bayan mika wa sarkin sandar da kwari da baka da butar goro na masarautar, gwamnan ya mika wa sarkin fatanya bisa al’adar masarautar.

  • Ambaliyar Ruwa: Ministar Jinkai Ta Kaddamar Da Rabon Tallafi Ga Mutum 5,428 A Neja

Gwamnan ya jayo hankalin sabon sarki ya yi amfani da kwari da bakar wajen tabbatar da tsaro da kare mutuncin masarautar, gwamnan bai tsaya nan ya janyo hankalin Attahiru II da ya yi a amfani da fataryan wajen dawo da martabar masarautar.
Gwamna Abubakar ya yaba wa sabon sarkin bisa jajircewa da hadin guiwar shugaban karamar hukumar, Hon. Isma’ila Musa Modibbo wajen tsayin daka duk da matsalar tsaron da masarautar ke fuskanta na ganin an dawo da zaman lafiya.

Ya jawo hankalin sabon sarkin da ya yi amfani da basirarsa wajen hada kan al’ummar masarautar, musamman a irin wannan lokacin da ake fuskantar matsalar tsaro da kuma siyasar da ake fuskanta, wanda hadin kan masarautar Kagara da zaman lafiya shi ne zai bai wa masarautar gagarumar ci gaba.

Haka kuma gwamnan ya ce gwamnatinsa na iya bakin kokarinta kuma ba za ta gaza ba har sai zaman lafiya ya dawo a masarautar ta yadda ‘yan gudun hijira za su samu damar komawa gidajensu.

Labarai Masu Nasaba

Bikin Nadin Sabon Sarkin Jere Na 11 Ya Kayatar

Dakta Olusola Saraki: Shekara 10 Da Rasuwar Dattijon Arziki, Baya Goya Marayu

A bayaninsa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar da ya samu wakilcin Mai Martaba Etsu Nupe, Dakta Yahaya Abubakar, shugaban majalisar sarakunan Neja, ya yi addu’ar Allah ya bai wa sabon sarki kwazo da muruwar jagoranci al’ummar kasar Kagara.

Ya bayyana zaben Attahiru II na kasar Kagara, zabi mafi cancanta, wanda dan lokacin da ya dauka kan karagar zuwa yanzu ya kawo sauye-sauye masu amfani da ci gaba a majalisar ta jiha.

Da yake bayanin karbar farar sanda ta azurfa daga hannun Gwamna Abubakar Sani Bello, Mai Martaba Attahiru II, Malam Ahmad Garba Gunna, ya gode wa gwamnan musamman a lokacin zaben sabon sarkin da bai tsoma bakinsa ba, wanda hakan ne ya karfafa guiwar masu zaben yin zabin da ya dace.

Sarkin ya ce tabbas kamar yadda ya yi rantsuwa zai kare martabar masarautar Kagara a matsayinsa na sabon sarkin, kuma ya kara karfafa guiwar al’ummar masarautar da cewa da yardarm Allah an kawo karshen rashin tsaro a kasar Kagara, noma da farauta za su dawo, ‘yan gudun hijira za su koma gidajensu, amma dole sai gwamnati ta kara karfafa guiwarta a kan matakan tsaron da take dauka.

Attahiru II ya gode wa majalisar sarakunan Neja bisa jagorancin Mai Martaba Etsu Nupe kan kwarin guiwa da shawarwarin da suke ba shi.

Daga cikin manyan sarakunan da suka halarcin bikin, sun hada da Sarkin Bichi na Jihar Kano, Mai Martaba Nasiru Ado Bayero, Sarkin Lafiya na Jihar Nasarawa, Mai Martaba Isma’ila Jibrin, sauran sun hada da sarkin Lafiagi da Patigi na Jihar Kwara, da sarkin Maradun na Jihar Zamfara.

Sarakunan Jihar Neja da suka hada da Mai Martaba Etsu Nupe, sarkin Minna, Etsu Agaie da Lapai, Bargu da Kontagora duk sun samu halarta, yayiN da sarkin Suleja ya samu wakilci kasancewar baya cikin kasar.

An haifi Malam Ahmad Garba Gunna ne ranar 1 ga watan Janairu ta shekarar 1975, a garin Yakila da ke gundumar Gunna daga gidan sarautar Gunna wanda jika ne ga Malam Attahiru na daya sarkin Gunna na sha biyar, wanda ya sarauci gundumar Gunna tsakanin 1928 zuwa 1954.

Ya gaji kakansa da aka daga darajar sarautarsa daga Dagacin Gunna zuwa Hakimin Gunna na sha tara.
Attahiru II, Malam Ahmad Garba Gunna, ya fara karatunsa na boko a makarantar faramaren da ke Gandun Albasa, zuwa makarantar sakandaren je ka dawo ta Sharada duk a Jihar Kano. Yana da darajar karatu ta HND daga kwalejin kimiyya ta Birnin Kebbi a fannin mulki da tsare-tsare, ya samu darajar karatu ta digiri a kan fannin lissafi a jami’ar Jihar Kwara.

Ya kuma samu digirin-digirgir a kan lissafi daga jami’ar Abuja. Inda ya yi hidimar kasa a Jihar Kwara.

Sabon sarkin Kagara, Ahmad Garba Gunna (Attahiru II) kafin nadinsa shi ne Dagacin Gunna kuma Danmajen Kagara. Ya kasance tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya goge a fannoni da dama a fannin kididdigar kudi da lissafi, mulki da tsare-tsare tafiyar da aikin gwamnati, wanda ya fara aiki da karamin ma’aikaci har ya kai babban matsayi a gwamnati Neja.

Tsohon shugaban hukumar tara haraji ne na gwamnatin jiha, kafin nan ya taba zama Cashier ma’aikatar kula da ma’aikatan jihar, ya taba zama Akanta ma’aikatar kula da asibitocin jiha, mataimakin Akantan ma’aikatar kimiyya da fasaha ta jiha. Inda daga bisani ya zama babban Akantan gidan gwamnatin jiha, kafin nadinsa shi ne shugaban hukumar tara kudaden shiga ta jiha.

Mai Martaba Attahiru II, yana da mata daya, Hajiya Rakiya Ahmad Muhammad, wadda cikakkiyar ‘yar boko ce mai darajar karatun digirin-digirgir a kan yanayin muhalli, kasancewarta matar basarake bai hana ta neman ilimi ba, yanzu haka tana da ‘ya’ya hudu da sabon sarkin.

Masarautar tana da ‘yan majalisa guda biyar da suka hada da Madakin Kagara, Alhaji Abubakar Jibo Garba, sai Barden Kagara, Alhaji Abubakar Awuri Giwa, da Tafidan Kagara, Alhaji Shahabudeen Isah, sai Walin Kagara, Ibrahim Shehu Kagara.

Masarautar Kagara na da iyaka da masarautar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna daga gabas masu arewa, Masarautar Minna daga gabas masu dama, Masarautar Kontagora daga Yamma.

Masarautar ta shahara ne a kan noma farautar da kasuwanci, tana da manyan fitattun ‘yan boko da suka taka fage daban-daban a aikin gwamnatin jiha da tarayya. Tana daya daga cikin masarautun da ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane suka addaba, kasancewar tana kunshe da dinbin ma’adinan kasa masu yawa da albarkar kasar noma.

Duk da cewar zuwa yanzu abubuwan sun fara daidaituwa sakamakon tsauraran matakan da gwamnatin jiha da tarayya da sabon sarkin da karamar hukuma ke dauka.

Kabilun sassan masarautar da ‘yan siyasa sun shirya gangami domin murna bikin irinsa na tarihi wanda ba a taba yin irinsa ba a tarihin masarautar ba.

ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yan Jarida Sun Karrama Mawallafin Blueprint, Mohammed Malagi

Next Post

Sharuddan Da ACF Ke Son Duk Mai Neman Ya Gaji Ganduje Ya Cika

Related

Bikin Nadin Sabon Sarkin Jere Na 11 Ya Kayatar
Masarautu

Bikin Nadin Sabon Sarkin Jere Na 11 Ya Kayatar

5 months ago
Dakta Olusola Saraki: Shekara 10 Da Rasuwar Dattijon Arziki, Baya Goya Marayu
Manyan Labarai

Dakta Olusola Saraki: Shekara 10 Da Rasuwar Dattijon Arziki, Baya Goya Marayu

6 months ago
Gwamnan Bauchi Ya Mika Wa Sarkin Katagum Sandar Girma
Masarautu

Gwamnan Bauchi Ya Mika Wa Sarkin Katagum Sandar Girma

7 months ago
Bagudu Ya Amince Da Nadin Sarakunan Gargajiya 2 A Masarautar Yauri Ta Jihar Kebbi
Masarautu

Bagudu Ya Amince Da Nadin Sarakunan Gargajiya 2 A Masarautar Yauri Ta Jihar Kebbi

7 months ago
Zabarmawa Sun Yi Gagarumin Taro A Kebbi
Masarautu

Zabarmawa Sun Yi Gagarumin Taro A Kebbi

9 months ago
Dakta Bashir Bala Getso Ya Zama Jakadan Hausawa
Masarautu

Dakta Bashir Bala Getso Ya Zama Jakadan Hausawa

9 months ago
Next Post
Hanya Mafi Sauki Ta Magance Matsalolin Sashin Shari’a – Ganduje

Sharuddan Da ACF Ke Son Duk Mai Neman Ya Gaji Ganduje Ya Cika

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Sojin Injiniya Ta Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Kasar Sin Ta Tallafawa Kongo Kinshasa Ta Fuskar Aikin Ceto

Tawagar Sojin Injiniya Ta Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Kasar Sin Ta Tallafawa Kongo Kinshasa Ta Fuskar Aikin Ceto

June 4, 2023
Ana Bin Jihar Kano Bashin Sama Da Naira Biliyan 240, Inji Abba Gida-gida 

Gwamna Yusuf Ya Kori Jami’an Cibiyar Alhazan Kananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

June 4, 2023
Me Ya Sa BRICS Ke Kara Samun Karbuwa Daga Kasashen Duniya

Me Ya Sa BRICS Ke Kara Samun Karbuwa Daga Kasashen Duniya

June 4, 2023
Sana’ar Kwalliya

Sana’ar Kwalliya

June 4, 2023
Ranar Muhalli Ta Duniya: Kwanturolan NIS Na Jihar Ribas Ya Gargadi Jami’ai Kan Gurbata Muhalli

Ranar Muhalli Ta Duniya: Kwanturolan NIS Na Jihar Ribas Ya Gargadi Jami’ai Kan Gurbata Muhalli

June 4, 2023
Mutane 18 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutane 18 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

June 4, 2023
Takaitaccen Tarihin Ka’idojin Rubutun Hausa (II)

Takaitaccen Tarihin Ka’idojin Rubutun Hausa (II)

June 4, 2023
Dalilin Da Manoman Rama A Jihar Katsina Ke Kara Habaka

Dalilin Da Manoman Rama A Jihar Katsina Ke Kara Habaka

June 4, 2023
Farashin Tumatir Ya Karye Bayan Ghana Da Kamaru Sun Turo Shi Kasuwannin Nijeriya

Farashin Tumatir Ya Karye Bayan Ghana Da Kamaru Sun Turo Shi Kasuwannin Nijeriya

June 4, 2023
Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Yawan Kyautarsa — Garba Shehu

Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Yawan Kyautarsa — Garba Shehu

June 4, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.