Gwamnatin Jihar Ebonyi ta bai wa jami’an tsaro umarnin harbe duk wani bata garin da aka gani yana dauke da bindiga ko kuma wani makamin hallaka jama’a domin kawo karshen kashe-kashen da ake samu a jihar.
Kwamishinan yada labaran jihar, Uchenna Orji, ya ce wannan umarnin ya shafi rundunar tsaron sa kai ta jihar da aka yi wa suna Ebubeagu, wadda ita ma aka bai wa jami’anta wannan dama na hallaka wadannan tsageru.
- ‘Yansanda Na Bincike Kan Cire Idon Wani Almajiri A Bauchi
- Bikin Kirisimeti: Wanda Takardun Fasfonsa Ya Kare Zai Iya Dawo Wa Gida – Gwamnati
Rahotanni sun ce daukar wannan mataki ya biyo bayan tashin hankalin da aka gani samu a Litinin, inda wasu tsageru dauke da makamai da ake zargin magoya bayan haramcacciyar kungiyar IPOB ne, suka kutsa kai cikin birnin Abakaliki suna harbe-harbe da rana tsaka.
Lamarin da ya razana mutanen garin wadanda suka rufe shaguna da kasuwanni da kuma bankuna.
Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun kai harin Abakaliki ne da zummar tabbatar da umarnin hana zirga-zirga na kwanaki biyar da shugaban wani sashe na kungiyar IPOB ya bayar.
Wannan hari ya yi sanadiyar hallaka wasu mutane tare da jikkata wasu da dama, duk da ya ke kwamishinan yada labaran jihar ya ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon harbe-harben.
Orji, ya zargi maciya amanar jihar da yada labaran tilastawa mutane zaman gida da zummar razana su domin ganin ba su gudanar da harkokin su na yau da kullum ba.
Kwamishinan, ya ce Gwamna David Umahi, ya kuma bai wa jami’an tsaron da ke aiki a jihar, tare da rundunar Ebubeagu umarnin ci gaba da sintiri a Birnin Abakaliki da kuma wasu biranen jihar domin tabbatar da tsaro.
Idan dai ba a manta ba, Simon Ekpa, daya daga cikin shuganannin da ke fafutukar kafa kasar Biyafara, ya sanar da cewar za su kaddamar da shirin zaman gida na tilas na kwanaki biyar daga ranar 9 ga watan Disamba zuwa 14, a ci gaba da fafutukar ganin sun cimma muradunsu.