Shugaban sashen kulla yarjejeniya da doka na ma’aikatar kasuwancin kasar Sin, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi amfani da tsarin WTO na warware takaddama, game da matakan da Amurka ta dauka kan fitar da sassan laturoni da sauran kayayyaki zuwa kasar Sin.
Shigar da karar da kasar Sin ta yi a gaban WTO, wata hanya ce da ta dace don warware batutuwanta ta hanyar doka, da kiyaye ‘yanci da moriyarta.
Jami’in ya ce, a cikin ‘yan shekarun nan, bangaren Amurka yana ci gaba da bayyana ra’ayin batun tsaron kasa, da yin amfani da matakan hana fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, da kawo cikas a harkokin cinikayyar sassan laturoni na kasa da kasa, da sauran kayayyakin da aka saba bisa al’ada, da yin barazana ga zaman lafiyar tsarin samar da masana’antu a duniya, da kawo cikas ga tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, da keta ka’idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, da keta muhimman ka’idojin tattalin arziki, da cutar da muradun zaman lafiya da ci gaban duniya, wanda hakan tamkar kariyar cinikayyar ce. (Ibrahim Yaya)