Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa manema labarai a yau Talata cewa, Sin na farin ciki ganin kasashen duniya, sun kara mai da hankali kan nahiyar Afrika, amma tana matukar adawa da mai da nahiyar fagen dagar yin takara, yayin da ake taron kolin Amurka da kasashen Afrika.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, ofishin nazarin tattaunawa tsakanin kasashen duniya na kasar Afrika ta kudu ya ba da rahoton cewa, gwamnatocin Amurka na yanzu, ko na da, ba su dauki matakan da suka dace wajen taimakawa kasashen Afrika ba, maimakon haka nufinsu shi ne amfani da karfin kasashen Afrika wajen takarar Sin da Rasha, da rage karfin wadannan kasashe biyu a Afrika da ma duniya. Amma, kowa ya san cewa, Sin ta kan dauki matsayin hana tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe, da hadin kai don cin moriya tare, matakin da ya samu karbuwa, da maraba daga kasashen Afrika.
Wang Wenbin ya ce, taimakawa bunkasuwar kasashen Afirka, nauyi ne dake wuyan kasashen duniya, kuma Sin na tsaya tsayin daka kan kulla sahihiyar hulda da kasashen Afrika, da hadin kai, da cika alkawari, da cin moriya tare, kuma tana nacewa ga kafa dangantaka ta mutunta juna, da nuna adalci da hadin kai. (Amina Xu)