Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, tsarin da ta kirkiro na fallasa masu wawure asusun gwamnati (Whistle-blowing) ya daina tasiri.
Gwamnatin ta kirkiro da wannan tsarin ne a ranar 21 ga watan Disambar 2016 domin ta bai wa ‘yan Nijeriya kwarin gwiwar sanar da bayanai ga gwamnati kan duk wani Jami’in gwamnati da take zargin ya wawure kudaden gwamnati bisa nufinta na yakar cin hanci da rashawa a kasar.
Har ila yau, a karkashin tsarin, gwamnatin na baiwa duk dan kasar da ya bayar da bayanai akan jami’an gwamnatin da suka saci kudaden gwamnatin wani kaso daga cikin kudaden daga kashi 2.5 zuwa kashi 5.
Ministar kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin kasa kasa Zainab Ahmed ce ta sheda wa manema labarai na fadar shugaban kasa hakan a yau laraba jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Ministar ta kara da cewa, gwamnatin tarayya ta kirkiro da wannan tsarin ne domin yakar cin hanci da rashawa a kasar nan, tare da kuma bayar da kariya ga rayuwar masu sanar da gwamnatin bayanai akan barayin na gwamnati.