Babban Sufeton Janar na ‘yansandan Nijeriya, IGP Usman Baba, ya gargadi dukkanin masu aika-aikar kai farmaki ga ofisoshin hukumar zabe ta kasa (INEC) a sassan kasar nan da cewa hukumar ‘yansanda ba za su taba lamuntar hakan ba kuma za su dakile duk wani harin da ake shirin kai wa ga ofisoshin INEC.
Shugaban na ‘yansandan ya kuma sake nanata yunkurin hukumar tare da yin hadaka da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da sahihi kuma ingattaccen zabe a 2023 kamar yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawari.
IGP ya shaida hakan ne a yayin ganawa da manyan jami’an ‘yansanda da suka kunshi kwamishinonin ‘yansanda dangane da batun zaben 2023 da ya gudana a shalkwatar rundunar da ke Abuja, ya ce, “Daga yanzu abun ya Isa haka. Wannan mummunar aika-aikar ba abun lamunta ba ne sam.”
Ya kuma ce, ‘yansanda sun fito da sabbin dabarun aiki bisa kwarewa wajen shawo kan matsalolin da ka iya tasowa a lokacin zaben 2023