Dakarun rundunar Hadin Kai (OPHK) tare da hadin gwiwar rundunar tsaro ta farin Kaya (CJTF) sun kashe ‘yan ta’adda 47 ciki har da manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram.
Rundunar hadin gwiwar tare da goyon bayan rundunar soji ta 21 ta Armored Brigade Bama, jihar Borno, sun kai farmakin ne kan daya daga cikin sansanonin ‘yan ta’addan da ake mata kirari da mahallaka a kauyen Gazuwa da ke karamar hukumar Bama a ranar 12 ga watan Yunin 2022.
Sansanin da ‘yan ta’addan suka sauya wa suna zuwa “Gazuwa ko Markas” daga wacce akafi sani da Gabchari, Mantari da Mallum Masari, tana dauke da mayakan boko haram sama da 3,000 da iyalansu daga bangaren Abubakar Shekau.
A cewar wani rahoton leken asirin da Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, ya bayyana wa LEADERSHIP, ya ce sojojin sun farma ‘yan kungiyar Boko Haram/ISWAP a yankin, inda suka yi artabu da su Na tsawon sa’o’i fiye da Uku.