Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da mutane 30 daga garin Garin Gidigore da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kauyen Garin Gidigore na da tazarar kilomita kadan daga garin Birnin Gwari a Jihar Kaduna, inda ‘yan bindigar ke da sansanoni da dama a dajin da ke makwabtaka da su.
An gano cewa, harin da ‘yan bindigar suka kai kauyen a daren ranar Litinin ya dauki tsawon sa’o’i da dama, inda kuma aka kona gidaje da dama yayin da suka yi awon gaba da kauyen baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp