- Muna Kokarin Warware Lamarin – INEC
- Mutum Miliyan 11 Na Fuskantar Kasa Yin Zaben 2023
Idan har gwamnatin tarayya ba ta dauki matakin gaggawa ba, to sama da masu zabe miliyan 11 na iya hana su zaben 2023 sakamakon karuwar rashin tsaro a yankin kudu maso gabas.
Alkaluma daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ya nuna cewa yankin kudu maso gabas na da yawan masu jefa kuri’a miliyan 10.9, yayin da aka samu karin 930,000 a sabon rajistan zabe.
Wadannan sabbin masu jafa kuri’a sun kasa fita domin amsar katunan zabensu a ranar farko sakamakon dokar hana zirga-zirga a duk ranar Litinin wanda kungiyar IPOB ta kakaba a yankin.
Hukumar INEC ta kasa gudanar da ayyukanta a Jihar Anambra sakamakon tsoro da jami’anta suke yi da masu amsar katunan jefa kuri’a na yuwuwar kai hari ga ‘yan daban da suka tilasta dokar zaman gida dole a gaba daya yankin kudu maso gabas a ranar Litinin.
Tun da farko dai, shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya kakaba dokar zaman gida dole a duk ranar Litinin a matsayin dubarar da zai ta tilasta wa gwamnatin tarayya ta saki.
Nnamdi Kanu, wanda ake tsare da shi a gidan yarin Kuje da yake jiran shari’ar da ake masa a kotu kan laifuka da suka shafi cin zarafin mutane, lalata tattalin arzikin kasa, kuntata wa mutanen yankin, karya dokokin kasa, tilasta dokar hana zirga-zirga, kai farmaki da kuma kashe mutanen da suka fita a ranar Litinin.
Binciken LEADERSHIP ya gano cewa amsar sabon katin zabe bai gudana ba a kananan hukumomi 21 da ke jihar, inda jami’an INEC da masu amsar katin zaben suka kaurace wa ofisoshin hukumar da ake raba katin zabe, saboda ana tsammanin ‘yan daba za su iya kai farmaki.
Wasu daga cikin wadanda suka yi rajistar zabe da aka tuntuba sun bayyana cewa sun gwammace su amshi katin zabensu a wata rana amma ba a ranar Litinin ba.
“Zan je in amsa katin zabena a gobe amma ba a ranakun Litinin ba, saboda ban san in hadu da farmakin ‘yan bindiga wadanda suke tilasta dokar zaman gida dole,” in ji wani wanda ya yi rajistar zabe da ya yi magana kan lamarin.
Lokacin da aka tantubi kwamishinar zaben Jihar Anambra, Misis Kueen Elizabeth Agwu ta bayyana wa LEADERSHIP ta wayar salula cewa ta kai jami’anta ofishinta domin gudanar da raba katun zabe. Ta ce ta kasa kula da yadda ake gudanar da rabon katin zabe saboda tsoron kai farmaki ga ‘yan daba masu tilasta dokar zaman gida dole.
“Na kira wasu daga cikin jami’aina da ke kananan hukumomin jihar sun bayyana min cewa suna kananan hukumomin domin rarraba katunan zabe, amma ni na kasa fita domin duba yadda aikin ke guda saboda tsoron farmakin masu tabbatar da dokar hana zirga-zirga a ranar Litinin.
“Kamar yadda tsarin yake, ni ba zan iya jibje jami’aina domin su rarraba sabon katin zabe ba, dole ne in kula da yadda aikin ke gudana wajen magance matsaloli da ka iya tasowa, amma kamar yadda kuke iya gani sakamakon lamarin da ake afkuwa a jihar na dokar zaman gida dole da aka kakaba a duk ranar Litinin ta sa na kasa fita.”
Shugabar INEC na jihar ta sha alwashin za ta zagaye jihar domin sa ido kan yadda rabon katin zaben ke gudana amma ban da ranakun Litinin.
Wasu daga cikin mutane da suka zanta da wakilinmu sun bayyana cewa suna tsoron fita daga gidagensu, saboda tsohon harbi wanda masu tilasta dokar hana zirga-zirga suka kakaba a wasu sassan Jihar Inugu a ranar Asabar da ta gabata.
Wani mazaunin kan titin Kenyatta, Obinna Ogbonna ya bayyana cewa ya yi kokarin zuwa ofishin INEC tun da safe amma bai ga kowa ba.
Sauran wadanda suka yi magana kan lamarin ga wakilinmu sun bayyana cewa ba za su iya zuwa ofishin INEC har sai wa’adin dokar zaman gida dole ta kare na kwanaki biyar.
Wani mamba a kungiyar farar hula da ke Inugu, Nwabueze Anoyua ya bukaci jami’an tsaro su yi kokarin samar da tsaro ga mutane domin samun nasarar wannan aiki.
A daidai lokacin da aka fara amsar sabon katin zabe a kasa, Jihar Imo na ci gaba da fuskantar kalubalan rashin tsaro da ke hana mutane fita domin amsar katin zabensu. Wannan lamarin yana shafar jami’an INEC da ke gudanar da aikin a irin wadannan jihohi. Mutane da kan iya ziyartar cibiyoyin INEC domin amsar sabon katin zaben, jami’ai kalilan ne ke iya sauraron su.
Da yake yi wa LEADERSHIP karin haske, Ikenna Uzondu ya nuna mamakinsa kan yadda ake fargaba wajen hana gudanar da aikin a wasu jihohin.
A cewarsa, karfin hali ne zuwa wurin amsar sabon katin zabe sakamakon yawaitar rashin tsaro da ke addabar jihar. Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar su dauki matakin gaggawa wajen hukunta wanda suke aikata wannan laifi.
A nasa jawabin, Dakta Jude Ohanele ya yi kira ga gwamnatin tarayya da samar da tsaro a dukkan ofisoshin INEC da ke fadin kasar nan. Ya kuma bukaci gwamnatin jihar ta samar da kungiyar sa-kai domin samar da tsaro a kananan hukumomin jihar.
Dakta Ohanele ya bukaci gwamnatin jihar da jami’an tsaro su yi amfani da basirarsu wajen bayyana wadanda suke aikata laifukan da suka addabi al’umma. Sannan ya yi kira da gwamnati ta samar da natsuwa a zukatan mutane domin ganin wannan aiki na amsar sabon katin zabe ya gudana yadda ya kamata.
Sai dai kwamitin yakin neman zaben Obi-Datti karkashin jam’iyyar LP ya bukaci jami’an tsaro su tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya ba a tauye musu damar hana su zabe ba sakamakon rashin tsaro.
A cewar kwamitin Obi, dole ne jami’an tsaro su tashi tsaye wajen yin aiki tukuro na tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun amsa katin jefa kuri’arsu.
Rahoton LEADERSHIP a kan fara bayar da sabbin katin zabe da INEC ta fara ya nuna cewa mafi yawancin mutane a yankin kudu maso gabas sun kaurace wa cibiyoyin amsar katin zabe sakamakon rashin tsaro.
‘Yan bindiga da ke yankin kudu masu gabas sun lalata mafi yawancin ofisoshin INEC wanda hakan ta sa mafi yawancin mutane sun kaurace wa ofisoshin musamman a ranakun Litinin saboda dokar hana zirga-zirga.
Da yake tattaunawa da LEADERSHIP, kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na
Obi-Datti wanda shi ne tsohon shugaban kungiyar hadakar jam’iyyu (IPAC), Dakta Yunusa Tanko ya bayyana cewa bai zai yuwu ba a hana ‘yan Nijeriya damar yin zabe ba sakamakon rashin tsaro.
“Yana da matukar muhimmanci mu yi kira ga jami’an tsaro su yi kokarin kare rayuwa da dokiyoyin al’umma kamar yadda tsarin mulki ya dora musu. Dole ne jami’an tsaro su tsare kowa lokacin amsar katin zabe. Ya kamata ‘yan kasa su fito domin kare ‘yancinsu. Muna ganin yadda ake kai farmaki kan ofisoshin INEC, amma duk da haka dole ne ‘yan kasa su fito su kare ‘yancinsu.
“Kamar yadda muka yi kira ga mambobinmu su dauki sha’anin tsaro da muhimmanci kuma su kare ‘yancinsu. Dole a tsare ‘yan Nijeriya kan abin da zai hana su damar yin zabe wanda ya shafi rayuwarsu. Domin haka, muna kira ga jami’an tsaro na kasa su tabbatar da cewa ba a tauye wa ‘yan Nijeriya hakkinsu ba,” in ji
Tanko
A wasu sassan kasar nan, amsar sabon katin zaben yana tafiya yadda ya kamata, yayin da yake samun jinkiri a wasu yankuna. A bangare daya kuma, an samu yawan masu amsa a wasu jihohin, yayin da a wasu kuma aka samu karancin masu amsar sabon katin zaben.
Alal misali, kamar a ginin kungiyar sarakunan gargajiya da ke Uyo inda ake amsar sabon katin zaben ana samun sauyin katin zaben a Uyo, yayin da aka samu karancin aikin a Akwa Ibom.
Bayan haka, an samu zanga-zanga a wasu wurare bayan da karfe uku na rana ta buga lokacin da INEC ta ayyana a rufe amsar katin zaben.
“Na zo wannan wuri tun da safe, amma aiki yana tafiyar hawainiya wanda ya tilasta min dole in koma ofis domin kulawa da wasu takardu, na dawo uku saura amma jami’an INEC sun bukaci in dawo gobe,” in ji Offiong Udoffot, wani ma’aikacin gwammnati yake fada wa wakilinmu.
Inemesit Akpan ta yi korafin yin kuskure a katinsa, “Katin da aka ba ni sunana daidai ne, amma ba hotona ba ne a ciki.
“Lallai ina so in yi zabe, amma saboda wannan kuskure da aka samu a halin yanzu, suna fada min cewa in jira zuwa 2027, domin babu abin da za su iya yi. Amma me ya sa INEC za ta yi irin wannan kuskuran sauya hoto?
Wasu daga cikin masu zanga-zangan sun bukaci INEC su kara lokacin yin aikin zuwa karfe hudu na yamma, domin samun damar bai wa masu zabe amsar sabon katinsu. A cewarsu, hakan zai iya hana wasu damar yin zabe.
Jami’in INEC ya yi ikirarin cewa, “Ba a amince mana mu yi magana ga manema labarai ba kan kuskuren suna da sauya hoto da sauran abubuwa da suke tattare da wannan aiki.”
“Sunana Silas daga gundumar ta daya har zuwa sashi na 30 an fada min ana ganin sunana, amma na je wurin ban gani ba, daya daga cikin masu zanga-zangan yake bayyana wa wakilinmu haka.
An samu karancin amsar sabon katin zaben a Jihar Ekiti kamar yadda ganau daga Ado Ekiti, Babban Birnin Jihar Ekita suna bayyana a ranar Litinin da ta gabata.
Wakilinmu wanda ya za ziyarci ofishin INEC da ke karamar hukumar Ado Ekiti, inda ya samu karancin masu amsar katin zaben. Ya ce akwai yawan jami’an INEC a ofishin wanda suke bai wa masu zaben katinansu.
Daya daga cikin jami’an zaben da ya yi magana kan lamarin ya bayyana cewa ba a amince masa ya fadi yawan adadin wadanda suka amshi katin zaben ba, amma an samu karancin masu amsa wanda ba ya kara karfafa masu kwarin gwiwa.
Ya ce, “Mun zo wannan wuri tun karfe 7:30 na safe muna jiran mutane su zo domin amsar sabon katin zabensu. Kadan daga ciki ne suka zo, wanda kusan kashi 95 ba su amsa sabon katin zabensu ba.
“Babban kalubalen da muke fuskanta shi ne, mutane ba sa zuwa da katin da aka ba su lokacin rajistar da kuma kuskuren bayanai.”
Wasu da suka yi rajistar a Jihar Kaduna wadanda suka kasa amsar katin zaben a rana ta farko sakamakon karancin man fetur da ya haddasa tsadar baban hawa.
Da yake zantawa da LEADERSHIP a Kaduna, daya daga cikin masu jefa kuri’a, Charles Alom, mazaunin Sabon Tasha ya ce, “A yanzu haka a Kaduna kudin sufuri ya lunka sakamakon karancin man fetur. A yanzu haka ban da kudin da zan biya na sururi domin amsar sabon katin zabena, amma dai zan je in amsa a wani lokaci saboda ina son yin zabe a 2023.”
Wani mai suna Adams Sule ya ce, “A yau ne aka fara amsar sabon katin zabe, zan amshi nawa amma ba yau ba duk lokacin da na samu dama zan je in amsa kuma zan yi zabe a 2023.”
Hukumar INEC ta bayyana yawan yawan mazabun da aka fi samaun yawan masu amsar sabon katin zabe da kuma wadanda aka samu karanci.
Mazauna Babban Birnin Tarayya (Abuja) sun fito kwansu da kwarkatansu wajen amsar sabon katin zabe a shalkwatan INEC da ke Area 10 a yankin Garki, domin amsar katin jefa kuri’a.
An bayyana cewa a ranar Litinin tun da misalin karfe takwas na safe, an samu sama da mutane 500 da suka fito daga kananan hukumomi shida na Abuja suna jiran a bude kofar shiga ofishin INEC.
Sakamakon yawan mutane a bakin kofar shiga ofishin INEC, jami’an tsaro suka ki bude kofa har sai da mutane suka fusata tare da yin barazanar balle kofar idan aka hana su amsar katin zabensu.
Sama da jami’an tsaro guda 20 suka yi kokarin shirya mutane ta yadda za su shiga cikin harabar ofishin ba tare da matsala ba har zuwa lokacin da za a fara bayar da sabon katin zaben.
Hakazalika, mazauna Ilorin da ke Jihar Kwara sun zo ofishin INEC da yawan gaske domin amsar sabon katin zabe. Haka kuma ofishin INEC da ke Akerebiata cikin karamar hukumar Ilorin ta gabas da kuma Bode- Saadu da ke karamar hukumar Moro sun cika makil da mutane domin amsar sabon katin zabe.
Ofisoshin INEC a Jihar Taraba musamman a Jalingo, Babbar Birnin jihar sun cika makil da jama’a masu karbar sabon katin zabe.
A ziyarar LEADERSHIP a sakateriyar karamar hukumar Jalingo, daya daga cikin cibiyoyin amsar sabon katin zaben ya cika da dandanzon al’umma domin amsar sabon katin zaben.
A kasuwar Ikot Ishie wurin da ofishin INEC yake a karamar hukumar Kalabar da ke Jihar Kuros Ribas da LEADERSHIP ta ziyarta, mataimakin daraktan na INEC, Mista Soni Ezuma ya bayyana cewa aikin yana tafiya yadda ya kamata.
A Jihar Benuwai, mafi yawancin mazauna jihar sun yi dafifi a ofisoshin INEC domin amsar sabon katin zabe, musamman ma matasa.
A Jihar Neja kuwa, an samu karancin masu amsar katin zaben a sakateriyar kananan hukumomin jihar, inda suka kunyata jami’an INEC da suke bayar da sabon katin zaben.
Jihar Katsina ce ta fi yawan masu amsar sabon katin zabe. Bincike ya tabbatar da cewa amsar sabon katin zaben ya fara ne tun daga ranar Litinin da ta gabata da misalin karfe 9 na safe har zuwa karfe 4, inda mazauna jihar suka cika ofishin INEC da ke fadin kananan hukumomi 34 na jihar.
Haka ma lamarin yake a can Jihar Kogi, inda aikin amsar sabon katin zabe ke tafiya cikin tsari tare da samun dinbin mutane.
INEC ba ta fara gudanar da aikin amsar sabon katin zaben a karamar hukumar Misau da ke Jihar Bauchi. Mazauna yankin sun bayyana cewa hukumar INCE a Misau ba ta fada musu ranar fara amsar sabon katin zaben ba.
Wani mazaunin Misau ya shaida wa LEADERSHIP cewa, “Bayan da mutane suka cika ofishin INEC da ke Misau domin amsar sabon katin zaben, jami’an INEC sun bayyana musu cewa aikin ba za a fara ba kamar yadda suka yi tsammani.”
Haka ma lamarin yake a Asaba, Babbar Birnin Jihar Delta ba a san ranar fara amsar ba duk da aikin amsar sabon katin na ci gaba da gudana a wasu yankuna.
A Jihar Ogun, tun kafin lokacin fara amsar sabon katin jami’an INEC ke fama da yawan jama’a a ofisoshinsu da ke Akomoje da Iyana Mortuary.
A daidai lokacin da LEADERSHIP ta ziyarci karamar hukumar Abeokuta a garin Akomoje, akwai yawan mutane masu amsar sabon katin zabe da suka yi dogon layi.
Daya daga cikin wadanda ba su amince da yadda aiki ke gudana ba, Ogunwusi Monsurat Abidemi ya zargi jami’an INEC da rashin shirya mutane duk da yawan zafin rana.
Wasu daga cikin jami’an INEC da suka tattauna da LEADERSHIP sun bayyana cewa hukumar INEC ta tsara amsar sabon katin zaben ne kamar yadda aka yi rajista a gundumomi. Sun ce rashin hakuri ne ke janyo matsalolin da ake fuskanta a wurin.
Jami’an INEC sun ce za su dakatar da aikin ne da misalin karfe 3 na rana kamar yadda hukumar ta ba su umurni tun daga Abuja.
Da yake zantawa da LEADERSHIP kan karancin jami’an INEC masu bayar da sabon katin zaben a wasu sassa, sakataren gangamin yaki da kare hakkin Dan’adam (CDHR), Kwamared Yinka Folarin ya bukaci hukumar INEC ta yi kokarin magance matsalar domin kar a hana wadanda suka cancanta damar jefa kuri’a a cikin kasar nan.
Sai dai hukumar INEC ta sha alwashin magance dukkan matsaloli da suke tattare da amsar sabon katin zaben.
A Jihar Zamfara, maza da mata ne ke ta tururuwa zuwa ofisoshin hukumar INEC domin amsar sabon katin zabe da a ka fara rabawa a ranar Litinin da ta gabata.
Daraktan yada labarai da wayar da kan al’umma a kan katin zabe na hukumar INEC a Jihar Zamfara, Ibrahim Bello ya shaida wa wakilinmu cewa yanzu haka hukumar ta tura sabon katin zaben a ofisoshinta na kananan hukumomi domin ba masu katin abun su.
“Muna da tabbacin cewa kowane ofishinmu a yanzu haka jama’a ne ke ta tururuwa domin amsar sabon katin zaben da aka fara rabawa.
Wata da take amsar sabon katin zabe a Gusau, Aisha Garba ta shaida wa wakilinmu cewa nata ya bace ne ta sabunta shi domin ta zabi wanda zai yi masu adalci ga ilimi ‘ya’yansu.
Shi kuwa, Mahe Musa ya bayyana cewa ya samu canjin gari ne daga Kaduna zuwa Gusau mahaifarsa shi ne ya gyara katinsa domin ya samu damar zabar wanda ya ke son ya mulke shi a 2023.
A ranar Litinin da INEC ta fara bayar da sabon katin zabe a fadin kasar nan, Jihar Kano kamar dai sauran jihohin ita ma an shelanta fara karbar sabon katin zaben, sai dai kuma akwai karancin fitowar jama’a a cibiyoyin karbar sabon katin zaben da ke fadin jihar.
Ana alkanta rashin fitowar jama’a domin karbar nasu sabon katin zabe da matsalar karancin man fetur wanda hakan ya haifar hauhawar farashin ababan hawa na haya da ma mallakar masu zaman kansu, sannan kuma a wasu wuraren an samu matsalar rashin isassun ma’aikatan da ake sa ran za su sauraron jama’ar da suka so domin sauke wannan nauyi.
Wani da wakilinmu ya samu zantawa da wani wanda ya ya bukaci a sakaya sunansa ya kasance makwabci ne ga wurin karbar sabon katin zabe, ya bayyana cewa shi ko biyo shi aka yi da katin ma ba zai karba ba, domin wadanda suka zaba a baya sun ci amfanarsu, don haka shi ba zai kara yin zabe ba.
A cewarsa, raka asara me da guda kawai a kan
Batun matsalolin sauya suna kowa a cibiyoyin karbar sabon katin zaben da aka fara samun korafi a kansu kuwa, wakilinmu ya yi dan tattakin domin tattaunawa da wadanda suka samu wannan matsana a nasu sabon katin zaben.
Wasu dai sun bayyana matsalar kuskuren sauyin suna ko hoto ko kuma wasu jawabai, yayin da wasu ba su hadu da irin wannan matsala ba.
Wasu sun bayyana cewa su dai sun yi nasara domin ba su gamu da irin wannan matsala ba.
Sai dai wakilinmu ya yi ta kokarin tattaunawa da wadanda suka sami matsaloli har zuwa lokacin hada wannan rahoton lamarin ya ci tura.
Assalamu alaikum
A harabar hukumar zabe ta Kano wato INEC da ke unguwar zoo road Gidan Buhari abin ya faru
Munje karbar katin zaben mu wanda suka sanar a Rediyo cewar Ranar 12/12/2022 Duk wanda yasan yayi katin zabe yaje a karbi nasa saboda haka gurin a cike yake da dan Adam daga kowace zaba ankafe hotunan wadanda katin su yazama Ready.
Anan wata mace ta ga nata saidai kuma hoton tane ajiki amma sunan banata bane Nan nace mata tashiga takai korafi yawan da akai yasa Security suka datse kofar suka hana mutane shiga sai dai daga kowace mazaba su kira mutane biyar in an gama dasu su sake kira ban san ya suka karke da matar Nan ba tanata fada.
Ni kuma gashi sun kafe hoto na da sunana amma an nemi nawa anrasa dana tambayesu.yaushe zan samu shine suka cemin wai saidai inyi hakuri Bayan Zabe inzo inkarba
Sai wasu suma su biyu maza suma ance sai bayan zabe abun daya dauremin kai shine taya zasu kafe hotunan mu kuma suce babu namu