An dakatar da Babban manajan darakta na hukumar bayar da tallafi ga wadanda suka yi asarar amfanin gona kamar yadda jaridar Daily Tust Saturday ta ruwaito.
Bayanai sun tabbatar da cewa, an tunbuke Aliyu Abdulhameed ne saboda yawan zarge-zargen da ake yi a kansa na cin-hanci da karbar rashawa wadanda suka hada da badakalar zunzurutun kudin da suka kai naira biliyan 5.6, a shekara ta 2018, kan noman alkama a jihar Kano da Jigawa, wadanda ake zargin jami’a hukumar ta NIRSAL da jefa wa a cikin lalitarsu.
Yadda rahoton jaridar Daily Trust ya tona asirin wata badakala a hukumar NIRSAL
A wani rahoton bincike da wannan jaridar ta wallafa a cikin watan Janairun bana wanda ta yi bincike a kan yadda bashin da aka ci na biliyoyin nairar da hukumar NIRSAL ta tsaya aka ci ga wasu kamfanoni guda uku domin yin noman rani a wata gona mai fadin hrkta 20,000 a jihar Kano da Jigawa wanda aka hada baki da jami’an hukumar ta NIRSAL.
Lokacin gudanar da bincike, jaridar DAILY TRUST ta ranar Lahadi,ta je garin da wannan abin ya faru, da ke jihohin arewa maso yamma, domin ji daga majiya mai tushe.
Shugabannin wannan al’umma, sun bayyana cewa, an gaya musu, an kikiro wannan shirin ne domin Tallafa wa kananan manoman da yawansu ya kai 20,000. Wasu daga cikin manoman sun ce, ba za su taba yafe wa ba, da yaudarar da aka yi musu. Bayan na bayar da gonata domin gudanar da wannan shiri, sun yi alkawarin za su ba ni taki, za kuma su haka min rijiya ko su taimaka min yadda zan jawo ruwa, amma ashe duk yaudara ta suke yi, ba su yi min komai ba.
Araya Alhaji Idi, wani shi ma daga cikin manoman, daya daga cikin manoman a garin Ringim da ke jihar Jigawa, ya bayyana cewa, tun da suka muka yi maga da su da farko ba su sake dawo wa ba, kuma ko ta waya ba su kira mu ba, domin sanar da al’umma halin da ake ciki ba, sun bar mu a igiyar ruwa. In ji shi.
Sai dai shugaban hukumar ta NIRSAL, ya musanta wannan zargin da ake yi masa, wanda ya ce, wannan turka-turkar da ta taso, wasu mutane ne daga gefe, kuma suke kokarin rura wutar riki domin su bata masa suna da kuma hukumar.
Sai dai idan muka lura da rahoton da jaridar DAILY TRUST ta bayar, ya sa, hukumar EFCC ta nemi Manajan daraktan tare da wasu ma’akatan na NIRSAL domin su yi bayani kan zargin da ake yi musu na mallake makudan kudi da sunan yin aiki, kuma ba a yi aikin ba.
Bayan binciken hukumar EFCC, ita ma hukumar ICPC da jami’an ‘yansanda su ma suna bincike a kan zargin da ake yi na badakalar wasu ayyuka.
An nemi shugaban ya je ya yi bayani, ranar Alhamis din da ta gabata jim kadan bayan kan wannan zargin da ake yi masa, sai dai har zuwa lokaci kammala wannan rahoto, bai mika matsayin nasa ga wani wanda zai ci gaba da tafiyar da aikin nasa ba, kafin a san cikakken halin da ake ciki.
An nemi jin da bakin shugaban ko kuma jami’in hulda da jama’a na hukumar, amma duka abin ya ci tura.
Wata majiyar labarai, mai tushe, ta nuna cewa, ba a kori Abdulhameed ba, sai dai ya dakata ne domin bayar da damar gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake yi masa, wanda hukumar EFCC da ta ICPC da kuma jami’an tsaro na farin kaya ke yi masa.