Hukumar Kwallon Kafa ta Kasar Argentina, ta ce a yau Talata za ta gudanar da bikin lashe kofin duniya da tawagar kwallon kafar kasar ta yi a ranar Lahadi.
Za a bikin lashe gasar ne a filin Obelisk da ke birnin Buenos Aires, inda aka saba gudanar da shagulgulan wasanni a kasar.
- Buhari Ya Ba Ni Tabbacin Za A Gudanar Da Sahihin Zabe A 2023 – Atiku
- Sin: Matakin Amurka Da Daukar Matsayar Kashin Kai Da Kariyar Cinikayya Na Yin Illa Ga Hada hadar Samar Da Hajoji
Bugu da kari, gwamnatin kasar ta ayyana yau Talata a matsayin ranar hutu, inda har bankuna ba za su yi aiki ba don nuna farin cikin lashe wannan kofi mafi daraja.
Hukumar kwallon kafar kasar ta ce a yau ne tawagar kwallon kafar za ta tashi zuwa wannan dandali na Obelisk don wannan biki.
Argentina ta doke Faransa da kwallaye 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan da suka tashi 3-3 a wasan da aka sanya a cikin jerin wasannin karshe mafiya kayatarwa da aka taba bugawa a gasar kofin duniya.
An yi ta sowa da murna a fadin Argentina sakamakon lashe wannan kofin da tawagar kwallon kafar kasar ta yi a karon farko cikin shekaru 36.