A jiya Litinin, cibiyar watsa shirye-shirye da harsunan kasashen Asiya da Afrika na babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG, ta gudanar da taron karawa juna sani, dangane da yanayin da kasar Sin ke ciki a kokarinta na dakile cutar COVID-19, ta kafar yanar gizo, a kasar Kenya, inda aka gayyaci ’yan jarida daga kasashen Kenya da Tanzania, da Uganda.
A yayin taron, daraktar ofishin hada shirye-shirye na sashen Kiswahili na CMG dake kasar Kenya Madam Du Shunfang, ta yi bayani kan nasarorin da kasar Sin ta samu cikin shekaru 3 da suka wuce, a kokarinta na yakar annobar COVID-19, da yadda kasar ta daidaita manufarta ta kandagarkin yaduwar cutar a kwanakin nan, bisa sabuwar damar da ta samu.
Gami da tasiri mai kyau da sabuwar manufar za ta yi wa mu’amalar da ake yi tsakanin bangarorin Sin da Afirka.
A nashi bangare, Eric Biegon, dan jaridar gidan telabijin na kasar Kenya, ya ce kokarin da kasar Sin ta yi a fannin dakile cutar COVID-19, ya samar da sakamako mai burgewa.
Yana kuma sa ran ganin farfadowar tattalin arzikin kasar Sin cikin matukar sauri a shekara mai zuwa, wadda a cewarsa, za ta amfani kasashen Afirka da duniya baki daya. (Bello Wang)