Babbar Tashar Talabijin ta duniya France 24 ta kulla alakar aiki tsakaninta da Qausain TV dake nan Nijeriya.
Shugaban Qausain TV, Malam Nasir Musa Idris (Albani Agege) ne ya bayyana haka a wannan makon, jim kadan bayan amsa gayyatar da tashar ta FRANCE 24 ta yi masa.
Nasir Albani wanda yanzu haka yana Kasar Faransa domin kammala shirye-shiryen fara aikin, ya ce “A halin yanzu ina Kasar Faransa, bayan da muka samu tagomashin gayyata zuwa birnin Faris (Paris) inda babban gidan talabijin mai kololuwar daraja wato FRANCE 24 ya ba ni kujerar zama daya daga cikin jajirtattun masu gidajen talabijin na duniya dake da alaka da su.
Ya kara da cewa wannan wani tafarki ne na habbaka daraja tare da watsa martabar harshen hausa a fadin duniya.
“Lallai alakar zumunci mai karfi ta kullu tsakanin Qausain TV da sahar FRANCE 24, kuma hadaka ce mai matukar alfanu da sauki da zata zama gadar sadar da hausawan duniya, domin kara sanin abubuwan da ke faruwa a duniya a saukake.
Qausain TV dai tashar Talabijin ce da ta yi fice a Nijeriya wajen yada shirye-shirye masu kayatarwa cikin harsunan Hausa, Turanci da kuma Larabci.