GABATARWA
Sanin kowa ne cewa yanar gizo ko “internet”, wata muhimmiyar kafa ce da ci gaban zamani ya kawowa bil adama, wanda ta tabbatar da babban sauyi da dan Adam ya samu a fannin fasahar sadarwa, kuma matakin da ya sauya yadda daidaikun mutane, da masana’antu, da kamfanoni, da gwamnatoci da sauransu ke gudanar da ayyuka da dama. Sabanin wasu fasahohi da su kan kebanci wasu kasashe, ko sassa na duniya su kadai, yanar gizo ta zo da wani sabon yanayi, ta yadda ta dinke duniya waje guda, har ma a kan ce duniya ta koma tafin hannu, ko duniya ta zama tamkar wani dan karamin kauye da kowa ya san kowa, duba da yadda na’urori masu kwakwalwa da ake amfani da su kan yanar gizon ke iya musayar bayanai daga dukkanin sassan duniya baki daya.
Yanar gizo na ci gaba da taka muhimmiyar rawa a kusan daukacin fannoni na ci gaban rayuwar bil adama, kama daga harkokin raya ilimi, kimiyya da fasaha, da bangarorin cinikayya da kasuwanci, da na gudanar da gwamnatoci, da tsaro, da sufuri, da aikewa da sakwanni, wasanni, da harkokin nishadantarwa, aikin likita, da na sama jannati da dai sauransu. To sai dai kuma duk da haka, a daya hannun yanar gizo na zama babbar barazana ta wasu faskokin, kasancewarta wata kafa da miyagu ke iya amfani da ita wajen musayar bayanai, ko tattara kudaden aiwatar da munanan ayyuka, na kungiyoyin ’yan ta’adda ko masu aikata muggan laifuka, irin su cinikayyar muggan kwayoyi, ko kutse da satar bayanai ta yanar gizo, ko hari kan hanyoyin sadarwa na akokan gaba ko takara, da leken asiri dai sauransu.
La’akari da hakan ne ya sanya a watan Nuwamba da ya shude, ofishin watsa bayanai na gwamnatin kasar Sin ya fitar da wata takardar bayani mai kunshe da manufofin kasar Sin, na cimma burin gina al’ummar duniya mai makoma guda a fannin cin gajiyar yanar gizo.
Ko shakka babu kasar Sin ta ci muhimmiyar gajiya daga hidimomin yanar gizo, tana kuma daukar matakai daban daban na bunkasa ci gaban fasahohin yanar gizo, da kuma manufofin kare ta. Ya zuwa yanzu miliyoyin Sinawa sun fahimci alfanun dake tattare da ma’amala da yanar gizo, suna kuma ci gaba da ba da gudummawa ga gina yanayi mai kyau na ci gaba da cin gajiya daga fasahohinta, bisa tsari na tsaro da zaman lafiya, da yin komai a bude, cikin hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa.
Matsaya Da Tanadin Kasar Sin Game Da Jagorancin Yanar Gizo
Yayin da tasirin amfani da yanar gizo ke kara shiga dukkanin sassan rayuwar bil adama, fannin lura da kare yanar gizo na kara fuskantar manyan kalubale. Don haka ne wannan takardar bayani da gwamnatin kasar Sin ta fitar a ’yan makwannin da suka gabata game da batun, ta yi fashin baki game da matakan shawo kan wadannan kalubale. Takardar ta bayyana aniyar kasar Sin don gane da ingiza matakan gina al’umma mai makoma guda a fannin cin gajiya daga yanar gizo, tare da fayyace matsayar kasar a fannin yaukaka hadin gwiwar kasa da kasa a wannan fage.
Karkashin manufofin kasar Sin a wannan fage, mahukuntanta na dora muhimmancin gaske kan ayyukan kyautata fasahohin yanar gizo, da hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa, ta yadda hakan zai wanzar da kyakkyawar gajiya da bil adama zai iya samu daga yanar gizo. Hakan ne me ya sa kasar Sin din ke ta bunkasa hanyoyin raya tattalin arziki masu nasaba da yanar gizo, da kyautata tsaron yanar gizo. Ana iya kuma ganin tasirin hakan a fannin ingancin hidimomi da kasar ke samarwa a fannin, matakin da masu fashin baki ke ganin ya share kyakkyawan fage na wanzar da ci gaba mai armashi, wanda kuma ya zamo ginshikin gina al’ummar bai daya mai makoma guda a fannin cin gajiya daga yanar gizo.
Kaza lika karkashin wannan manufa, ta gina al’ummar bai daya mai makoma guda a fannin cin gajiya daga yanar gizo, kasar Sin ta dukufa wajen samar da manyan ababen more rayuwa, da na’urorin aiki, da manhajojin da ake bukata domin cimma nasara.
Bugu da kari, kirkire-kirkire ta fuskar fasahohin sadarwa, sun haifar da bunkasar sabbin masana’antu, da sabbin kasuwanni, da sabbin dabarun gudanar da sana’o’i, yayin da dukkanin sassan ke kara hadewa da tsarin tattalin arzikin kasar, matakin da ke ingiza ci gaban kasar zuwa sabon matakin samun wadata.
Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, ya zuwa shekarar 2021, darajar sashen tattalin arzikin kasar Sin mai nasaba da fasahohin sadarwa, ya kai kudin kasar Sin yuan tiriliyan 45.5, adadin da ya kai kaso 39.8 bisa dari na jimillar mizanin awon tattalin arzikin kasar ko GDP, kuma hakan ya nuna cewa, sashen ne ke jan ragamar ci gaban tattalin arzikin kasar cikin sauri.
Cikin shekaru da dama na baya bayan nan, sashen tattalin arzikin kasar Sin mai nasaba da fasahohin sadarwa ya kasance na biyu mafi girma a duniya. Karkashin hakan, kasar ta fadada samar da na’urori da injuna da ake bukata a fannin, inda sakamakon hakan, ya zuwa watan Yunin shekarar nan ta 2022, adadin masu amfani da kafofin yanar gizo a kasar Sin ya kai biliyan 1.05, yayin da yanar gizo ta shiga kaso 74.4 bisa dari na sassan kasar. Kuma adadin turakun yanar gizo mai karfin 5G ya kai miliyan 1.85 a sassa daban daban na kasar. Kana Sin tana da masu amfani da wannan fasaha ta 5G a kan wayoyinsu na salula da yawansu ya kai miliyan 455.
A daya bangaren kuma, Sin din ce ke kan gaba wajen yawan adadin turakun na 5G, inda ta zama ta daya a duniya a fannin mallakar fasahohi da dabarun aiwatar da fasahohin yanar gizo na 5G.
Moriyar Da Al’ummar Sin Ke Samu Daga Yanar Gizo
Kasar Sin ta yi nasarar gina tsarin amfani da yanar gizo mafi inganci, da nufin amfanar rayuwar al’umma. Hakan wani bangare ne kuma na cimma nasarar da kasashen duniya suka sanya gaba, karkashin muradun ci gaba mai dorewa na MDD nan da shekarar 2030, wanda hakan ya yi daidai da burin kasar ta Sin, na sanya muradun al’umma gaban komai. Don haka dai mahukuntan kasar suka dukufa wajen ilmantar da al’ummar kasar game da alfanun dake tattare da yanar gizo a sassa daban daban na bunkasa rayuwa, ciki har da hidimomin lafiya, da yaki da fatara da sauran su.
Kari kan hakan, gwamnatin kasar Sin tana da dokoki na kare hakkin masu amfani da yanar gizo, da na hukunta masu aikata laifuka masu alaka da fasahar, dukkanin wadannan dokoki an tanade su musamman, domin tabbatar da ana amfani da yanar gizo bisa tanadin doka da oda.
Ko shakka babu tsaron yanar gizo na da matukar muhimmanci wajen dakile nau’o’in laifuka da a kan aikata ta wannan kafa. Don haka har kullum, kasar Sin ke baiwa fannin karfafa tsaro, da na tattara bayanai, da na kare abubuwan da al’umma ke dorawa ko musayar su kan yanar gizo matukar muhimmanci.
Gudummawar Kasar Sin Ga Hadin Gwiwar Duniya A Fannin Cin Gajiya Daga Yanar Gizo
Bisa jawaban da muka gabatar a sama, don gane da irin gajiyar da bil adama zai iya samu daga fasahohin yanar gizo, da kuma burin kasar Sin na ganin an kafa wani managarcin tsarin hadin gwiwa, wanda zai haifar da kafuwar al’ummar duniya mai makomar bai daya a fannin cin gajiya daga yanar gizo, muna ina fahimtar dalilan gwamnatin kasar Sin na yawaita tuntubar sassan masu ruwa da tsaki daban daban, take kuma yin hadin gwiwa, da raba ribar da ta samu da sauran kasashen duniya a wannan fanni. Kasar Sin ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da daidaikun kasashe, da yankuna daban daban, da ma gudanar da tattaunawa a matakin kasa da kasa ta fuskar tabbatar da nasarar kare yanar gizo daga harin bata-gari. Kaza lika kasar Sin na maida hankali matuka ga gudanar da shawarwari, da musayar kwarewa a fannonin raya tattalin arzikin yanar gizo, da aiwatar da sauye-sauye, da wanzar da ci gaban matakan jagorancin yanar gizo na bai daya, domin bunkasa harkar tsakanin kasa da kasa. Dukkanin wadannan fannoni, sun taimaka kwarai da gaske wajen gina al’ummar duniya mai makomar bai daya a fannin cin gajiya daga yanar gizo.
Kamar yadda na tabo batu a baya, don gane da muhimmancin kare yanar gizo daga miyagu da bata-gari, kasar Sin ta tanadi manufofi da dama na kulla hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa a wannan fanni, kamar dai yadda wannan takardar bayani ta fayyace, ciki har da batun fadadawa, da gudanar da ayyuka tare da sauran sassan kasa da kasa ta fuskar kandagarki, da dakile laifukan da ake yi ta yanar gizo, kamar zamba, da kutse domin satar bayanai ko leken asiri da dai sauran su.
Wannan muhimmin bangare ya kunshe ayyuka da dama, da suka hada da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin baiwa muhimman na’urori da ake bukata domin wanzar da hidimomin yanar gizo kariya, da tabbatar da daidaito a fannin tsare-tsaren ayyuka masu nasaba da fasahohin yanar gizo. Kari kan haka, akwai hadin gwiwa wajen yaki da ayyukan ta’addanci da ake kitsawa ta amfani da yanar gizo, kamar horas da ’yan ta’adda ko tattara kudade, ko ma watsa akidun ta’addanci ta wannan kafa. uwa uba akwai kuma ayyukan da suka shafi raba moriyar yanar gizo da sauran sassan duniya, kamar yadda a lokuta daban daban, kasar ta Sin ke samar da tallafi na kafa turaku, ko cibiyoyin samar da sadarwar yanar gizo a wurare daban daban na kasashe masu tasowa, matakin da ya yi daidai da ajanda ta 9 ta wanzar da ci gaba mai dorewa da majalissar dinkin duniya ta tsara, wadda ta tanadi bunkasa masana’antu da habaka kirkire-kirkire.
Rufewa
A wannan zamani da muke rayuwa cikinsa, kafar yanar gizo ta zamo tamkar gida guda da daukacin bil adama ke rayuwa a cikin sa. Dukkanin mu muna musayar alfanun wannan kafa, tare da fatan hakan zai bude mana karin kofofin shawo kan matsalolin mu na yau da kullum, tare da bunkasa harkokin ci gaban rayuwa a dukkanin fannonin ta. Don haka yunkurin kasar Sin na gina tsarin amfani da yanar gizo mai tsaro, budadde, bisa tsari, cikin hadin gwiwar dukkanin sassa, muhimmin jigo ne na bunkasa wayewar kan bil adama, kuma buri ne na dukkanin kasashen duniya bai daya.
Kuma a wannan zamani mai cike da kalubale, da kuma fatan samun ci gaba, takardar bayanin da kasar Sin ta fitar mai kunshe da manufofin kasar na cimma burin gina al’ummar duniya mai makoma guda a fannin cin gajiyar yanar gizo, za ta zamo wani mafari na yaukaka hadin gwiwar kasashen duniya, ta yadda za su yi aiki tare, a bude bisa doka, ta yadda za su ci gajiyar bai daya bisa daidaito. (Saminu Alhassan)