Mai Martaba Sarkin Gumel, Alhaji (Dakta) Muhammed Ahmed Sani na II, a madadin masarautar Gumel ya mika ta’aziyyar masarautar game da rasuwar Sarkin Lakwaja, Alhaji (Dakta) Muhammadu Kabir Maikarfi na III, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranan Laraba, 28 ga watan Satumbar 2022, bayan ya shafe shekaru fiye da 30 yana sarauta.
Babban dan Sarkin Gumel kuma Ciroman Gumel, Farfesa Lawal Ahmed Sani wanda ya jagoranci tawagar masarautar ta Gumel a madadin Sarkin wajen kai ziyarar ta’aziyya zuwa fadan Sarkin Lakwaja, ya bayyana rasuwar Sarki Kabir Maikarfi a matsayin babban rashi ga al’ummar masarautar da kuma iyalansa.
- Shugaba Xi Ya Tattauna Da Manyan Jami’an Gudanarwar Yankunan Hong Kong Da MacaoÂ
- Kirisimeti: Gwamnatin Bauchi Ta Raba Kayan Abincin Miliyan 145 Ga KiristociÂ
Ya ce masarautar Gumel ta kadu matuka a yayin da ta samu labarin rasuwar Sarkin Lakwaja, wanda ta bayyana shi a matsayin mutum mai kima da daraja a idonun al’ummarsa da kuma masarautun arewacin Nijeriya a tsawon shekaru fiye da talatin da ya yi a gadon sarautar Lakwaja.
Sarkin ya kara da cewa masarautar Gumel za ta dade tana jimamin rasuwar Sarkin Lakwaja, Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi III.
“A madadin masarautar Gumel, ina mika ta’aziyyata ga gwamnatin Jihar Kogi da majalisar sarakunan Jihar Kogi da majalisar masarautar Lakwaja da daukacin al’ummar masarautar Lakwaja da kuma iyalan marigayi sarkin a bisa wannan babban rashi.
“Ubangiji Allah ya jikansa da rahama ya sa Aljannati Firdausi ya zama makomarsa,” in ji Sarki Sani.