Gobara ta kone wani katafaren gini a karamar hukumar Hadejia da ke Jihar Jigawa.
Wani mazaunin garin ya shaida wa Leadership Hausa cewa lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi, inda gobarar ts lalata shaguna da dukiyoyi na miliyoyin Naira.
- An Raya Hadin Gwiwa Bisa Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Yadda Ya Kamata A Shekarar 2022
- Xi Ya Jaddada Bukatar Kare Lafiya Da Tsaron Jama’a
Kakakin hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya (NSCDC), a jihar, CSC Adamu Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da karfe 3:00 na dare a Nane Plaza da ke kan titin Kano zuwa Hadejia.
Ya yi bayanin cewa shaguna 28, motoci biyu, da babura biyu da aka ajiye a cikin harabar wurin da lamarin ya shafa ne suka kone.
Adamu ya ce ba a yi asarar rai ba, amma gobarar ta cinye dukiyoyi na miliyoyin Naira.
Ana binciken musabbabin faruwar lamarin.