A wani rahoton bincike da babbar hukumar bunkasa harkokin kasuwanci ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, galibin kamfanonin kasashen waje dake kasar Sin, suna goyon bayan managartan matakan yaki da annobar COVID-19 da bunkasuwar tattalin arzikin kasar a shekarar 2023.
A cewa majalisar bunkasa harkokin cinikayya ta kasa da kasa ta kasar Sin (CCPIT), daga cikin kamfanoni fiye da 160 na ketare, da cibiyoyin kasuwanci, da kungiyoyin da aka yi nazari kan su, kashi 91 cikin 100 na nuna goyon baya matuka ga managartan matakan yaki da annobar COVID-19 na kasar Sin.
Rahoton CCPIT ya kara da cewa, sama da kashi 99 cikin 100 na kamfanonin kasashen waje da aka yi nazari a kansu sun amince da hasashen tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2023, yayin da kashi 98.7 cikin 100 suka ce, za su ci gaba da fadada jarinsu a kasar Sin.
Bugu da kari, a cewar rahoton, kashi 89.8 cikin 100 sun bayyana cewa, za su kiyaye tsarin masana’antu na cikin gida na samar da kayayyaki, yayin da kashi 10.2 cikin 100 na shirin dawo da masana’antun ketare zuwa kasar Sin.
Mai magana da yawun CCPIT Yang Fan, ta bayyana cewa, kamfanonin kasashen waje da aka gudanar da nazarin a kansu sun bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da juriya, kuma yana da damar yin takara a fagen kasuwa, da tsarin masana’antu, kayayyakin more rayuwa, da yanayin kasuwanci mai kyau.(Ibrahim)