A yayin da duniya ta yi harama da shirye-shiryen tarbar sabuwar shekarar miladiyya ta 2023 da wasu kudurori da suka sa a gaba, ita kuwa Nijeriya ta sha damarar tarbar shekarar ce da harkokin siyasa na kakar zaben 2023.
A yanzu haka dai kwata-kwata abin da ya rage na lokacin gudanar da zaben na 2023 bai wuce makonni takwas ba.
- Zan Fi Mayar Da Hankali Kan Ilimi Da Matasa – Kwankwaso
- Kotu Ta Sake Hana DSS Cafke Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
Duk da cewa manyan yankunan siyasa shida da ke fadin kasar kowa na da muhimmiyar rawa da zai taka wajen tabbatar da nasarar dan takara a zaben shugaban kasa, amma kallo ya koma kan arewa maso yammacin Nijeriya, kasancewar yankin a matsayin “haa-babba” wajen yawan kuri’u da masu kada kuri’a.
‘Yan takarar guda hudu a manyan jam’iyyun siyasa sun kara tsananta kokarinsu wajen ganin kowani daya daga ciki ya doke dan’uwansa domin zama angon Nijeriya a zaben 2023.
A daidai lokacin da ‘yan takarar shugaban kasa suka kara jan damara, yanyin arewa maso yamma ya kasance sabon fagen yaki ga dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da na jam’iyyar APC, Bola Tinubu da takwaransa na LP, Peter Obi da kuma na NNPP, Rabiu Kwankwaso.
A kasa da watanni takwas da ya rage na gudanar da zabe, tuni alkaluma suna fara sauyawa a fagen harkokin siyasa. An samu karin zumudi ga ‘yan Nijeriya ganin suna da yawan zabi fiye da zaben 2019.
Ba kamar zaben 2019 ba, lokacin da ya kasance takara ne kawai a tsakanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Atiku, amma a zaben 2023 zai kasance ne a tsakanin manyan ‘yan takara guda hudu.
Yankin arewa maso yamma wanda ya tattara jihohin Kaduna, Sakkwato, Katsina, Kano, Kabbi, Zamfara da Jigawa yana da masu jefa kuri’a guda miliyan 22 wanda ya zarce sauran yankuna da ke fadin kasar nan, kuma wannan ne ya sa yankin ya kasance sabowar amarya, saboda a nan ne za a iya raba gardama a tsakanin manyan ‘yan takara, yayin da wani ya zama shugaban kasa saura kuma su kasance mafiya.
A dukkan wadannan jihohi guda bakawai, gwamnonin suna kan wa’adin mulkinsu na biyu, Jihar Zamfara ce kadai gwamnanta yake kan wa’adi na farkon mulki, inda wasu daga ciki suke neman takarar kujerar majalisar dattawa.
Gwamnan Jihar Zamfara ne kadai yake kokarin neman sake komawa kujerar gwamna daga cikin wadannan gwamnonin jihohin yankin arewa maso yamma. An dai tabbatar da cewa wasu daga cikin wadannan gwamnoni ba su tsaya takara a zaben 2023 ba, yayin da kalilan ne ke neman kujerar sanata.
Wannan lamari yana da matukar bai wa Atiku, Tinubu da Kwankwaso kalubale wajen ganin sun yi aiki tukuru domin samun damar lashe yankin arewa maso yammacin Nijeriya.
Haka kuma yankin yana fama da matsalar rashin tsaro wanda zai yi wa ‘yan takarar wahalar gudanar da yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali. Daga karshe dai, duk dan takarar da ya samu nasarar lashe wannan yankin da gagarumar rimjaye shi ne zai ci zabe a 2023.
Wata majiya da ke kusa da daya daga cikin ‘yan takarar ta bayyana cewa yankin arewa maso yamma yana da matukar muhimmanci, kuma kowani daya daga cikin wadannan manyan ‘yan takara guda hudu suna kokarin samun nasarar lashe zabe da kuri’u masu yawa a wannan yankin. Majiyar ta kara da cewa an tabbatar da cewa duk wanda ya samu nasarar lashe wannan yankin da gagarumin rinjaye, to shi ne zai zama shugaban kasan Nijeriya a 2023.
Atiku, Tinubu, Obi da kuma Kwankwaso dukkansu ba su da dama iri daya, amma dukkansu za su iya samun nasara, musamman idan aka je zagaye na biyu wanda masana ke ganin cewa zai yi wahala hakan ba ta kasance ba.
Jihar Kano ce ke da yawan kuri’u a yankin, ana ganin cewa za a fafata ne a tsakanin Tinubu na jam’iyyar APC da kuma Kwankwaso na jam’iyyar NNPP a wannan jiha.
A makon da ta gabata, Tinubu ya yi saurin garzayawa wurin Shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja domin ya yi masa yakin neman zabe a Katsina da Kano.
Gwamnan Jihar Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya siffata yankin arewa maso yamma a matsayin fagen yakin samun nasarar shugaban kasa a 2023.
Ganin rashin nuna jajircewar Kwankwaso wanda ya kasance dan asalin Jihar Kano, gwamnan Jihar Sakkwato ya bayyana cewa tun da babu wani dan takarar shugaban kasa daga yankin arewa maso yamma da ya yi tsaya-tsayin-daka, manyan jam’iyyu ne za su mamaye yankin.
Tambuwal ya kara da cewa yankin ya kasance fagen fafatawa ga jam’iyyu domin samun yawan kuri’un masu jefa kuri’a. Ya ce yankin ne zai fayyace wanda zai zama shugaban kasa a 2023.
An Tsaurara Matakan Tsaro A Ofisoshin INEC
A daidai lokacin da zaben 2023 ya rage saura kasa da wata biyu, an tsaurara matakan tsaro a dukkan ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke fadin kasar nan.
An dai jibge jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yansanda da jami’an fararen huda (DSS) da jami’an NSCDC, yayin da wasu jihohin ma har da jami’an sa-kai domin tsare gini da jami’an INEC da sauran muhimman kayayyakin zabe da aka fara rarrabawa.
Bincike ya nana cewa dukkan oshisoshin INEC da ke fadin kasar nan ya cika da jami’an tsaro na hadin gwiwa domin tsaurara matakan tsaro daga ‘yan daba da masu kone-kone wadanda suke kaddamar da hare-hare a ofisoshin wajen lalata ginin hukumar da tarwasa kayayyakin zabe.
A makon da ya gabata, Babban sufetan ‘yansanda na kasa, Mista Alkali Baba ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda ba za su taba bari a ci gaba da farmakar ofisoshin INEC ba. Ya ce ‘yansanda sun dauki matakai masu tsauri wajen tsare ofisoshin INEC da ma’aikatan hukumar a fadin kasar nan.
A Jihar Imo wanda lamarin ya fi zafi, lokacin da LEADERSHIP ta kai ziyarar gani da ido a ofishin INEC, ta samu an jibge jami’an hadin gwiwa da suka hada da na ‘yansanda da sojoji da DSS da kuma NSCDC, domin kare ofisoshin daga farmakin ‘yan ta’adda.
Wannan na zuwa ne kasa da awonni 24 bayan da wasu ‘yan daba suka lalata ofishin INEC da ke karamar hukumar Isu, wanda ya kasance farmaki na hudu da aka kai wa ofishin a Jihar Imo a cikin kasa da makonni uku. Sauran farmakin sun hada da na kananan hukumomin Orlu da Oru ta yamma da kuma shalkwatan INEC da aka kone a Owerri.
Da yake zantawa da wakilinmu, kwamishinan zabe na Jihar Imo, Farfesa Sylbia Agu ya bayyana cewa lallai an girke jami’an tsaro a ofisoshin INEC wadanda suka hada da ‘yansanda, sojoji, DSS da kuma NSCDC.
A nasa jawabin, kakakin rundunar ‘yansandar Jihar Imo, Michael Abattam ya bayyana cewa an tsaurara matakan tsaro na hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin shirin ko-ta-kwana.
A Jihar Inugu nan ma lamarin ba ta canza zani ba, inda LEADERSHIP ta binciko cewa jami’an hadin gwiwa sun mamaye shalkwatan INEC da ke Inugu, domin tsare jami’an INEC da sauran muhimman kayayyakin zabe.
Tun da farko dai, ‘yan ta’adda da ake zaton ‘yan kungiyar IPOB ne sun farmaki shalkwatan INEC da ke Inugu. Inda suka kone wani bangaren ginin tare da banka wuta a kan motocin hukumar.
Jim kadan bayan kai wannan farmaki, gwamnan Jihar Inugu, Ifeanyi Ugwuanyi ya gyara ofishin. A yanzu haka dai an jibge jami’an tsaro a gaba daya ofisoshin INEC da ke jihar.
A Jihar Kuros Riba wanda har yanzu ba a taba samun farmaki a ofisoshin INEC a jihar ba, shi ma an tsarorara matakan tsaro domin tsare muhimman kayayyakin zabe.
Kakakin rundunar ‘yansandar jihar, Irene Ugbo ya bayyana cewa ‘yansanda suna iya bakin kokarinsu domin tsare kayayyakin INEC daga farmakin ‘yan ta’adda.
Babban jami’an hulda da jama’a na Jihar Kuros Ribas, Anthonia Nwobi ya bukaci mazauna jihar da su tsare katin jefa kuri’unsa, domin samun damar yin zabe a 2023.
Domin tunkarar farmakin ofisoshin INEC a fadin kasar nan, an tsaurara matakan tsaro a ofishin INEC da ke Jihar Sakkwato domin kare muhimman kayayyakin zabe. An dai jibge jami’an tsaro da suka hada da ‘yansanda da sojoji da DSS da kuma NSCDC a gaba daya hanyar shiga harabar ofisoshin INEC da ke fadin Jihar Sakwwato.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar Sakkwato, Mohammed Usaini Gumel ya bayyana wa LEADERSHIP cewa rundunarsa ta dauki tsauraran matakai wajen shawo kan kalubalen tsaro a jihar, domin samar da cikkaken zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jihar.
A Jihar Kwara, ‘yansanda da jami’an NSCDC suna shafe awonni 24 wajen yin santiri a ofisoshin INEC da ke Illorin da dukkan kananan hukumomi da ke fadin jihar.
Kakakin hukumar INEC Jihar Kwara, Bolaji AbdulKadir ya tabbatar da jibge jami’an ‘yansanda da jami’an NSCDC a dukkan ofisoshin INEC da ke cikin jihar.
Haka lamarin yake a Jihar Neja, inda aka tsaurara matakan tsaro a ofishoshin INEC a fadin jihar, musamman ma a shalkwatan hukumar da ke Minna. An bayyana cewa jami’an ‘yansanda 10 aka jibge da kuma sauran jami’an tsaro da ke sintirin a shalkwatan hukumar INEC.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun ya bayyana cewa rundunarsa ta bi umurnin babban sufetan ‘yansanda wajen bayar da umurnin tsaurara matakan tsaro a ofisoshin INEC a fadin kasar nan.
Ya kara da cewa kwamishinan ‘yansandan Jihar Neja, CP Ogundele J. Ayodeji ya umurci jami’an ‘yansanda a jihar su gaggauta kawo dauki wajen tsare ofisoshin INEC daga duk wata farmakin ‘yan ta’adda.
Duk da yakin Boko Haram na tsawon shekaru 12 a Jihar Borno, ba a samu kai farmaki a ofisoshin hukunmar INEC ba a halin yanzu, ban da wanda aka taba samu a shekaru uku da suka gabata.
Idan ba a manta ba dai, an kai farmaki a ofishin INEC da ke Monguno a 2019, lokacin da ‘yan ta’adda suka kai farmaki a shalkwatan karamar hukumar. Haka kuma a tsakanin 2011 zuwa 2012, ‘yan ta’adda sun kai farmaki ofishin INEC da ke karamar hukumar Jere da ke cikin jihar.
Rundunar ‘yansandan Jihar Benuwe ta jibge jami’an ‘yansanda a fadin ofisoshin INEC da ke kananan hukumomi 23 domin tsare rayuka da kuma dokiyoyin hukumar zabe.
Kakakin hukumar INEC na jihar, Terkaa Andyar shi ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu ta wayar salula. Ya kara da cewa an jibge jami’an ‘yansanda da na NSCDC a gaba daya ofisoshin INEC da ke kananan hukumomi 23, domin dakile duk wata farmakin ‘yan ta’adda.
Shi ma kwamishinan ‘yansandan Jihar Benuwe, CP Wale Abass ya tabbatar wa mutanen Jihar Benuwe cewa za a tsare rayuka da dukiyoyinsu gabanin zabe da kuma bayan zaben 2023.
An dauki tsauraren matakan tsare ofisoshin INEC a Jihar Ekiti, domin tsare ofisoshin INEC da kayyakin zabe daga farmakin ‘yan ta’adda. An dai jibge jami’an ‘yansanda da sojoji da NSCDC a fadin ofisoshin INEC da ke fadin kananan hukumomi 14 a jihar.
Da yake zantawa da LEADERSHIP, Kakakin ‘yansandan Jihar Ekiti, Mista Sunday Abutu ya ce an tsaurara matakan tsaro a ofisoshin INEC da ke fadin jihar.
Hukumar INEC a Jihar Filato ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin gudanar da sahihin zabe.
A Jihar Kebbi, jami’an ‘yansanda guda 500 aka jibge a ofisoshin INEC da ke fadin kananan hukumomi 21 da kuma shalkwatan da ke Birnin Kebbi.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Nafi’u Abubakar shi ya tabbatar wa LEADERSHIP hakan a Birnin Kebbi.
Kakakin hukumar INEC na jihar, Abubakar Wala ya bayyana wa wakilinmu cewa hukumarsa ta gamsu da yadda aka jibge jami’an ‘yansanda da sojoji da DSS da kuma NSCDC a dukkan ofisoshin hukumar da ke fadin jihar.
Binciken LEADERSHIP ya tabbatar da cewa ba a taba samun farmakin ‘yan ta’adda a ofisoshin INEC ba a fadin kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.