Kakakin gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai zaman kanta ta kasar Sin, Xu Guixiang, ya bayyana a jiya cewa, yawan audugar da jihar ta samar a bana, ya kai ton miliyan 5.391, wanda ya karu da ton dubu 262 bisa na shekarar bara, kana adadin ya ci gaba da karuwa, bisa adadin jimillar audugar da baki dayan kasar Sin ke samarwa, wato ya kai kashi 90.2 cikin dari, wanda ya kai matsayin koli a tarihi, kana ana sayar da karin audugar ga sassa masu bukata.
Xu Guixiang, ya bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka gudanar a birnin Beijing, inda ya ce kasar Amurka, ta gabatar da dokar dakile yin aikin tilas ta Uygur, wadda karkashin ta aka yi zargin cewa, ana yin aikin tilas wajen noman auduga a Xinjiang, amma fa yunkurin Amurka shi ne haifar da illa ga nomawa, da fitar da audugar jihar, don haka dai dokar ba ta da amfani ko kadan.
Kaza lika kasar Amurka, ba ta amfani da audugar da ake samarwa a jihar Xinjiang, don haka babu bukatar sayar da audugar gare ta, kuma akwai al’ummu da dama a duniya, dake bukatar audugar Xinjiang, don saka tufafi da barguna, wanda hakan ke nuna cewa audugar jihar na da babbar kasuwa. (Zainab)