Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kara jaddada cewa babu wata kafa na yin magudin zabe a 2023.
A cewar hukumar, magudin zabe zai yi matukar wahala sakamakon yadda hukumar da shirya tsaf wajen gudanar da sahihin zabe a 2023.
- Ba A Aiwatar Da Wasu Matakai Na Yaki Da COVID-19 Domin Muzgunawa Al’ummar Uygur Ba
- Nijeriya Za Ta Fara Fitar Da Shinkafa Zuwa Masar
Sabuwar kwamishinar zaben Jihar Ebonyi, Misis Onyeka Ugochi ita ta bayyana hakan a Abakaliki lokacin da take zantawa da ‘yan jarida da kungiyoyin fararen hula.
“Magudin zabe ba zai taba kasancewa ba daga bangaren INEC. Sai dai magudin zabe ya kasance ta bangaren ‘yan siyasa. Mun yi iya bakin kokarinmu wajen tsare muhimman abubuwa kamar fitar da takardar sakamakon zabe da sauran abubuwa.
“A yanzu haka tsarin yana da matukar yi musu wahala wajen yin magudi sakamakon yin amfani da na’urar tantance masu jefa kuri’a. Ba za a iya tsallake na’urrarmu ba ko kuma har a iya kashe dukkan naurar da muke amfani da su lokacin gudanar da zabe.
“Yana da matukar wahala a iya yin magudin zabe a yanzu. Wannan lokaci ne da ‘yan jarida da kungiyoyin fararen huda za su yi aiki kafada da kafada wajen tsaftace al’umma. A bayyane muke gudanar da ayyukanmu, za mu yi iya bakin kokarinmu wajen ganin komi ya tafi yadda aka tsara.
“Za mu mayar da dukkan abubuwan da muka rasa a lokacin farmaki. Yana da matukar muhummanci ‘yan jarida su mara mana baya wajen gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata,” in ji ta.
Kwamishinar da ce a daidai lokacin da ‘yan jarida suke da rawar da za su taka na sanar da ‘yan kasa kan gasa a tsakanin jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da kuma manufofinsu, haka kuma suke da shi wajen fadakar da mutane domin amsar katin zabe kafin lokacin gudanar da zaben 2023.
Ta kuma jaddada wa ‘yan jarida da kungiyoyin fararen hula da sauran kawaye da kuma daukacin mutanen Jihar Ebonyi cewa a karkashin kulawarta hukumar za ta gudanar da sahihin zabe da zai kubuta daga rikice-rikicen zabe a jihar.