Kakakin gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai Xu Guixiang, ya ce ko alama, zargin da majalissar Turai ta yi cewa wai gwamnatin kasar Sin ta yi amfani da matakan yaki da annobar COVID-19, da nufin muzgunawa ‘yan kabilar Uygur a Xinjiang ba gaskiya ba ne. Xu ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.
Jami’in ya kara da cewa, yana fatan sassan kasa da kasa ba za su amince da wannan zance maras tushe ba, domin kuwa annobar COVID-19 da ta barke a watan Agusta a Xinjiang, wani batun kiwon lafiya ne mai tsanani dake bukatar matakan gaggawa. Xu ya ce a lokacin, cutar ta rika yaduwa cikin sauri, ta kuma harbi mutane masu tarin yawa, ta yadda shawo kan ta ya zamo abu mai matukar wahala a jihar ta Xinjiang, kuma hakan ya yi tasiri ga lafiya, da tsaro, da yanayin ayyuka da zamantakewar al’ummar jihar.
Kaza lika, a yayin da aka yi fama da wannan batu, dukkanin sassan hukumomin Xinjiang, sun dora muhimmancin gaske ga tabbatar da kyautatuwar rayuwar al’umma, sun saurari ra’ayoyin kalibu daban daban dake jihar, sun kuma aiwatar da tsare-tsaren shigar da albarkatun gona ko ina, an kuma yi aiki tukuru wajen warware matsalolin al’umma na gaggawa, kamar fannin samar da abinci, da tufafi, da matsugunnai, da harkokin sufuri, da kiwon lafiya da samar da magunguna, kana an yi namijin kokari wajen kare rayukan daukacin al’ummun kabilun dake jihar.
Bugu da kari, Xu ya ce ba yadda za a yi a gane wurin da annobar za ta bulla, balle a ce an cutar da wata kabila ta hanyar aiwatar da matakan dalike cutar. Don haka dai ba wani batu mai alaka da muzgunawa kabilar Uygur, kuma majalissar Turai, ta kirkiri wannan zargi ne da mummunar manufa, wanda hakan ya sabawa hankali. (SAMINU ALHASSAN)