Shugaban kasar Saliyo Leone Julius Maada Bio, ya jinjinawa kyakkyawar alakar dake tsakanin kasar sa da Sin, yana mai cewa sassan biyu sun shafe gwamman shekaru suna inganta dangantakar dake tsakanin su.
Shugaba Maada Bio, ya yi tsokacin ne a jiya Laraba, yayin da yake karbar sabon jakadan kasar Sin a Saliyo Wang Qing a fadar gwamnati. Ya ce “Gwamnati na tana martaba dangantakar dake tsakanin ta da Sin. A lokacin da ake tsaka da fuskantar barkewar annobar COVID-19, gwamnati na ta samu tallafi daga Sin. Kasar mu ta amfana sosai daga alaka, da cudanya da Sin. Muna godiya matuka da hakan”.
Kaza lika, shugaba Bio ya jaddadawa jakada Wang cikakken goyon bayan gwamnatin sa a fannin bunkasa alakar dake tsakanin sassan biyu.
A nasa bangare, jakada Wang ya ce kasashen Sin da Saliyo, sun amfana daga kyakkyawan kawance, karkashin manufar nan ta gina al’umma mai makomar bai daya. Ya kuma bayyana kwarin gwiwar samun cikakken hadin kai daga gwamnati da al’ummar Saliyo a yayin wa’adin aikin sa. (Saminu Alhassan)