Yana daga cikin abubuwan da aka ruwaito kan yafiyar Annabi (SAW), yafewarsa ga Bayahudiyar nan da ta sa masa guba cikin naman akuya, da aka kama ta ta ce, tana sane ta sa gubar da nufin cewa; In Annabi (SAW) sarki ne kawai, ya mutu a huta, in kuma da gaske Annabin Allah ne, Ubangijinsa zai kiyaye shi.
A wata ruwaya, Annabi ya sa a kashe ta sabida akwai wani sahabi da ya ci kuma ya rasu nan take. Ingatattar ruwaya ita ce, Annabi (SAW) ya yafe mata amma sabida mutuwar wani daga cikin Sahabbansa bayan cin gubar, Annabi (SAW) ya sa a kashe ta.
An ruwaito kuma cewa, Annabi (SAW) bai hukunta wani matsafi (Labidu) da ya yi masa tsibbo ba. Labido shi ne matsafin da ya yi wa Annabi (SAW) tsafi, wata rana ya ji jikinshi babu dadi kamar an kukkule shi, bayan ya kwanta bacci, sai ya yi mafarki da Mala’iku biyu, daya ya tsaya a wurin kai dayan kuma ya tsaya a wurin kafafunsa, sai daya ya tambayi daya, wai me ke faruwa da wannan Mutumin? Sai ya ba da amsar cewa, Asiri aka yi masa, waye ya yi masa? Labidu dan La’asa, a ina ya boye sihirin? A cikin rijiyar banu Zarwana, Meye maganin Sihirin? Ya karanta Suratu Falaki da Nasi. Take Manzon Allah (SAW) ya farka, ya aiki Sayyadina Aliyu da Zubairu bin Awwam, ya ce su shiga cikin rijiyar su dauko sihirin, Sayyadina Ali ne ya shiga cikin rijiyar ya dauko sihirin, an ruwaito cewa, sabida tsabar dafin sihirin duk Ruwan rijiyar ya zama kalan ja, kamar Ruwan lallen da mata ke kwalliya da shi.
Sai ya daura wani katon dutse akan sihirin. Bokan ya zana mutum-mutumin Annabi (SAW), ya tsitstsira allura goma sha daya (11) sannan ya hada da gashin Annabi (SAW) ya daure a duk gabobin mutum-mutumin da ya zana na Annabi (SAW). Bayan dawowarsu wurin Annabi (SAW) sai ya karanta Falaki da Nasi, kowacce Aya in yakaranta sai gashin ya warware, Annabi (SAW) ya ce sai na ji kamar an kwance ni a cikin Mari. Shi ma Annabi (SAW) ya yafe masa.
Haka nan kuma, Annabi (SAW) bai kama Abdullahi bin Ubayyu ba (Shugaban Munafukai) da sauran munafukai duk da mugayen maganganun da suke gaya masa “la’in raja’ana ilal Madinati, layukrijannal a’azzu minhal azal… in mun dawo gida Madina, sai masu girma sun kori kaskantattun daga cikin Madina”. Allah ya ba su amsa da cewa “wa lillahil izzatu wa lirasulihi wa lil muminina wa lakinnal munafikin la ya’alamun”, girma na Allah ne da Annabinsa da Muminai sai dai su Munafukai ba su sani ba”. Manzon Allah (SAW) ya gaya wa wasu daga Sahabbansa da suka ce Annabi (SAW) ya kashe Munafukai cewa, in ya kashe su za a koma ana cewa ya fara kashe Mutanensa, babu wanda zai lura da laifin da suka yi.
An karbo Hadisi daga Anas bin Malik (Khadimin Annabi (SAW) fiye da Shekara 10) yana cewa, sabida Albarkar hidimar da ya yi wa Annabi (SAW), sai da ya binne ‘ya’ya 100 ban da wadanda suka rayu, sannan kuma Allah ya ba shi dimbin dukiya ga zinarai ba adadi da gonakai da gidaje.
Anas yana cewa, wata rana Ina tare da Annabi (SAW) yana yafe da mayafi mai kwarin gefe (cin baki) sai wani Balaraben kauye ya zo ya fuzgo mayafin daga jikin Annabi (SAW) har sai dai shaidar fizga ta fito a wuyan dokin Annabi (SAW) sannan kuma Balaraben kauyen ya ce, Ya Muhammadu ka daura min dukiyoyin Allah (Zakkah) da ake ba ka a kan Rakumana guda biyun nan sannan kuma ba burge ni ka yi ba sabida ba kudinka ba ne, na Allah ne ake tarowa, sai Annabi (SAW) ya yi shiru sannan ya ce “wallahi dukiya ta Allah ce, haramun ne ni na ci, amma ni bawansa ne, ni dan rabo ne, dukiya ta Allah ce kuma zan ba ka, ni kuma kana so a saka min a kan abin da ka yi min?” sai ya ce, A’a, sai Annabi (SAW) ya ce masa sabida me? Sabida ba ka rama mummuna da mummuna, sai (SAW) ya yi murmushi ya ba da umurnin cewa, a daura wa Rakumi daya buhunan Alkama iya karfin rakumin sannan a daura wa dayan buhunan Dabino iya karfin rakumin.
Sayyada A’isha tana cewa, ban taba ganin Annabi (SAW) yana fadar kare wa kansa ba kan wata cuta da wani ya yi masa sai dai in an keta alfarmar Allah. Duk soyayyar da Annabi (SAW) ke yi wa Mu’azu bin Jabal amma da ya zagi Bilal a gabansa, sai da Annabi (SAW) ya ce masa “Mu’azu har yanzun akwai halin Jahiliyya a tare da kai”. Khalid bin Walid ya nemi taba wani daga cikin Sahabbai, sai Annabi (SAW) ya ce masa “kar wani don ya musulunta jiya ya ce zai taba min wani daga cikin Sahabbaina,” duk wannan don taba alfarmar Allah ne Annabi (SAW) ke shiga ciki ya rama.
In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne.
An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje.
An kama wani Mutum da yake shirin kashe Annabi (SAW), aka gurfanar da shi gaban Annabi (SAW), sai jikinsa ya fara makyerkyata, Annabi (SAW) ya ce masa, kar ka firgita, ko da ka yi niyyar kashe ni, Allah ba zai dora ka a kaina ba.
Zaidu dan Sa’anatal Yahudi ya zo wurin Annabi (SAW) kafin ya Musulunta yana neman Annabi (SAW) ya biya shi bashin da ya karba a wurinshi. Sai ya fizgo rigar Annabi (SAW) daga kafadarsa, ya shake kwalar Annabi (SAW) sai ya ce “Ku ‘ya’yan Abdulmudallib taurin bashi ne gare ku,” sai Sayyadina Umar ya tamka masa da magana mai kaushi, shi kuma Annabi (SAW) yana ta Murmushi, Annabi (SAW) ya ce ya Umar “Da ni da mai amsar bashi, mun fi bukatar wani abu ba irin wannan yadda ka yi ba,” cewa za ka yi “Ya Muhammad, ka dinga kyakkyawan biyan bashi, shi kuma ka ce masa, ba a haka ya dace a dinga zuwa karbar biyan bashi ba,” sauran kwana uku lokacin biyan bashin ya yi. Sai Annabi (SAW) ya umarci Sayyadina Umar da ya biya masa bashin sannan kuma ya kara masa loka Ashirin na hatsin sabida tsorata shi da ya yi, sai wannan ya zama sanadin Musuluntar Bayahuden.
Yadda labarin yake shi ne, wannan Bayahude yana daga cikin manyan malaman Yahudawa, ya kasance yana cewa, tun da ya ga fuskar Annabi (SAW) ya ga alamun Annabtarsa duka sai guda biyu ne kadai bai jarraba ba, su ne: Hakurinsa yana riga fushinsa, tsananin wautar masu wauta ba ta fusata shi sai dai ta kara masa hakuri.
Sabida in tabbatar da wannan ya sa na je don in gwada shi, sai kuma na tabbatar da hakan kamar yadda Attaura ta fada. In ji Malamin Yahudawan (dan Sa’anata)
Hadisai da suke magana kan hakuri da afuwar Annabi (SAW) lokacin da yake da cikakken iko kan komai wurin zartar da hukunci, ya fi karfin a ce za a zo da su baki daya.
Amma ya isa ma’auni a ce cikin Kabilar Kuraishawa ya taso kuma ya fara kira da a bi Ubangiji a cikinsu, wautar Jahiliyya a fili take a cikinsu har Allah ya taimake shi ya dora shi a kansu kuma ya hukunta shi a kansu.