Hukumar lafiya ta kasar Sin (NHC) ta bayyawa cewa, kasar Sin ta ba da rahoton halin da ake ciki game da COVID-19 a kasar, yayin da jami’ai da kwararru kiwon lafiyar kasar, suka halarci wani taro ta yanar gizo tare da hukumar lafiya ta duniya (WHO) da kasashe mambobinta jiya Alhamis.
Hukumar lafiyar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, a yayin taron, jami’ai da kwararru daga jami’ar Southeast sun ba da rahoto kan sabbin matakan rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta dauka, da yadda ake sanya ido kan sauyawar nau’in kwayar cutar, da kokarin yin allurar rigakafi da kuma jinyar masu kamuwa da cutar.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)