Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), ta karbu kyautar Naira miliyan 500 daga Gidauniyar Raya Afirka ta Abdulsamad Rabi’u, wadda ta ke taimakawa don tsaro da inganta rayuwar al’umma.
Kungiyar ta bayar da tallafin ne domin karfafa wa hukumar guiwa kan irin nasarorin da ta cimma wajen kyautata tsaro a bangaren shige da fice a Nijeriya da kuma matakin kasa da kasa.
- Cutar Murar Tsuntsaye Ta Barke A Jihohi 28 – Gwamnatin Tarayya
- ‘Yansanda Sun Kwato Makamai Da Dala 255,000 A Kwara
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwar da DCI Tony Akuneme, kakakin NIS, ya fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta kara da cewa, a wani taron amsar wasikar tallafin da aka shirya a hedikwatar hukumar da ke Abuja, Kwanturolan hukumar, Isah Jere Idris, ya jinjina tare da yaba wa shugaban rukunin kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Rabi’u bisa tallafin da kuma ganin irin kwazon ayyukan hukumar.
Ya jaddada aniyar hukumar na kara azama wajen inganta tsaro a Nijeriya.
Ya kuma tabbatar da cewar tawagar za su yi amfani da kudaden ta hanyoyin da suka dace domin kwalliya ta ci gaba da biyan kudin sabulu.
An samar da gidauniyar ne a ne domin taimaka wa da karfafa bangaren tsaro da inganta ci gaban kasashen Afirka.
Hakan wani shiri ne na kokarin shugaban rukunin kamfanin BUA da ke yi wajen tabbatar da ingancin zaman lafiya da tsaro a kasashen Afrika tare kuma da bunkasa ci gaban al’ummar kasashen nahiyar.
Idan za a iya tunawa, duka a kokarin hukumar NIS a bangaren inganta aiki da kula da sashen shige da fice a 2022, Kwamitin Fadar Shugaban Kasa kan Harkokin Kasuwanci (PEBEC), ya karrama NIS da lambar yabo a matsayin hukumar da ta fi kwazo cikin ma’aikatun Gwamnatin Tarayya cikin watanni bakwai.
Jagoran Gidauniyar, ‘Abdul Samad Rabiu Initiative for Africa’, Ubon Udoh ne, ya jagoranci tawagar zuwa hedikwatar hukumar NIS domin mika kyautar.