Jami’an diflomasiyyar kasashe sama da 130 dake kasar Sin, sun yaba da matakan yaki da COVID da kasar ta aiwatar, yayin wani taron fadakarwa game da manufofin yaki da annobar da ya gudana a ranar Juma’a.
Jami’an sun bayyana tsauraran matakan shige da ficen al’umma da Sin ta aiwatar, yayin da ake tsaka da fuskantar bazuwar annobar a matsayin wadanda suka wajaba, kuma aka gudanar da su kan lokaci, ta yadda suka haifar da wani sabon karsashi ga farfadowa, da ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.
Yayin taron, wanda sashen harkokin kasa da kasa na kwamitin kolin JKS, ya shiryawa manyan jami’an diflomasiyyar kasashen waje dake kasar Sin, mai ba da shawara ga ofishin jakadancin kasar Malawi dake Sin Fredrick P. Malire, ya ce Sin ta yi iyakacin kokarin ta, wajen kare rayukan jama’a da lafiyar su, cikin shekaru 3 da suka gabata, kuma daidaita matakan yaki da annobar da a yanzu Sin ta yi, za su kyautata hadin gwiwar gudanar da matakai tsakanin kasar da sauran kasashen duniya, ta yadda hakan zai share fagen farfadowa, da ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.
Jami’in na Malawi ya kara da cewa, kasancewar kasar Sin ta biyu a duniya a fannin karfin tattalin arziki, kuma muhimmiyar abokiyar huldar cinikayya da kasashe masu tarin yawa, sabbin matakan yaki da cutar da ta fitar, za su ingiza yawan cinikayyar kasa da kasa, wanda kuma hakan kyakkyawan labari ne ga kasashen duniya.
A nasa tsokaci kuwa, jakadan kasar Aljeriya a Sin Hassane Rabehi, cewa ya yi akasarin kasashe masu tasowa, sun samu tallafi mai matukar amfani daga kasar Sin, ciki har da alluran rigakafin cutar. Wanda hakan ya baiwa al’ummun su zarafin kimtsawa fuskantar annobar.
Don haka a cewar sa, Sin ta yi aiki tukuru, wajen tallafawa sassan kasa da kasa yaki da annobar, yayin da JKS ta himmatu wajen goyon bayan ci gaban daukacin bil adama. (Saminu Alhassan)