ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ina Mafita Game Da Ƙalubalen Ƙarancin Abinci A Nijeriya

by Ra'ayinmu
1 year ago
Abinci

A yayin da Nijeriya ke ci gaba da fuskantar dimbin matsalolin tattalin arziki da kuma kalubalen kare muhalli, wani sabon rahoto da aka fitar ya nuna cewa, ana kuma fargabar fuskantar matsalar karancin abinci a kasar, wadda kuma za ta iya jefa miliyoyin ‘yan kasar a cikin yunwa da rasashin samun abinci, mai gina jiki.

Wani rahoto na watan Fabirairu zuwa na Maris da masu fashin baki a CH suka fitar ya nuna cewa, daga watan Yuni zuwa na Agustan 2025, akalla ‘yan Nijeriya miliyan 30.6, cikinsu har da ‘yan gudun hijira a jihohin kasar 26 har da Abuja, za su iya fusakantar karancin abinci da kuma rashin samun abinci mai gina jiki.

  • Duk Da Dokar ‘Yancin Samar Da Abinci: Yara Miliyan 11 Na Fama Da Ƙaranci Abinci A Nijeriya
  • Ranar Mata Ta Duniya: Kalubalen Da Mata Ke Fuskanta A Siyasar Nijeriya

Adadin wannan alkaluman sun nuna cewa, an samu ‘yar raguwar da ta kai miliyan 33.1 a watan Nuwambar 2024, inda wannan lamarin ke da matukar bukatar masu ruwa da tsaki su smar da daukin gaggawa domin lalubo da mafita kan wannan matsalar.

ADVERTISEMENT

Wannan rahoton ha hadaka a tsakanin Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci da kuma Hukumar Samar da Abinci da ke a Majalisar dinkin Duniya FAO tare da hadin guwair sauran abokan hadaka, sun yi dubi a kan yanayin karancin abinci da Nijeriya za ta iya fuskanta.

Kazalika, duba da yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasar, a wasu yankunan kasar ana ci gaba da fuskantar gaza samun iya cin abinci, saboda yadda a yankunan, ake ci gaba da fusnatar barazar rashin tsaro, kalubalen sauyin yanayi da kuma kalubalen sauye-sauyen tattalin arziki.

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Jihohin da wannan matsalar ta fi shafa sun hada da, Zamfara, Borno, Yobe da kuma Katsina, musamman duba da yadda aukuwar yawan rikice-rikice, ya tarwatsa rayuwar miliyoyin alumomin yakin da fadawa cikin kangin fatara da yunwa da kuma rashin samun wadataccen abinci.

A ra’ayin mu, matsalar karancin abinci a kasar nan, ba boyayayen abu bane, musammamn duba da cewa, yawan aukuwar tashe-tashen hankula, kalubalen rashin tsaro da matsatin tattalin arziki, suna manyan hummulhaba’isin da ke janyo karancin abinci a a cikin alumma.

Misali, yawan samun hare-haren ‘yan bindiga a yankin kudu maso gabas, ayyukan ‘yan bindiga daji a yankin arewa masu yamma da kuma rikice-rikicen kabilanci a sauran yankuanan, sun janyo tarwatsa miliyoyin alumomi daga matsugunan su, lalata gonakansu wanda hakan ya janyo, aka samu raguwar noma amfanin gona, sauyar da amfanin gonar, inda hakan ya kuma haifar da karancin abinci a cikin alumma tare da samun hauhawan farashin kayan abinci.

Akasarin fannin noma a kasar nan, ya dogara ne kachokam kan samun ruwan damina, inda kuma fanin ke cin karo da samun sauyin yanayi, wanda hakan ke sanya wa a fusaknaci fari ko sauyin samun yanayin saukar ruwan sama da kuma akuwar annobar ambaliyar ruwan sama, inda hakan ke yiwa amfanin gona da aka shuka illa da kuma shafar dabbobi.

Wannan matsalar ta ambaliyar ruwansaman ba wai ta tsaya a kan amfanin gona bane, ta na kuma lalata matsunan alumma da kuma kara haifar da talauci a tsakanin su.

Sauye-sauye na dogon zango kan tattalin arziki da Gwamnatin Tarayya mai ci ta kirkiro da su a shekarar 2024 ta kuma wanzar da su, sun kasance za su iya janyo nakasu, a yunkurin da ake yi na samar da wadataccen abinci a kasar nan.

Duba da yadda ake ci gaba da samun hauhawan farashin kaya, karyewar darajar Naira, samun karuwar farashin man fetur, hakan yakara haifar da tsadar noma amfanin gona, tsadar sufuri, wanda hakan zai kara sanya wa masu sayen kayan abincin, su saya da tsadar gaske.

Bugu da kari, matsain na tattalin arzikin ya kuma janyowa alumma rashin samun wasu abubuwa kamar na iya kula da kiwon lafiyarsu da ci gaba da daukar nauyin karatun ‘ya’yansu.

Hukumar FOA tare da sauran masu ruwa da tsaki da suka hada da sasshen samar da abinci na Majalisar dinkin Duniya wato WFP da Asusun tallafawa kanannan yara na Majalisar dinkin Duniya UNICEF, Gidanuniyar Kula da kananan Yara da kuma kungiyar Kare Raji ta Mercy Corps, sun jima suna jaddada mahimmancin daukar matakan gaggawa na jin kai kafin aukuwar dukkanin wata annoba.

Daga cikin sakamkon taro na CH da aka gudaanr a Abuja wakilin FOA Nijeriya Kouacoau Dominikue Koffy ya jabawa Gwamnatin Tarayya da kuma masu ruwa da tsaki a CH, musamman bisa mayar da hankali da suka yi wajen ganin an samar da wadataccen abinci da kuma sanya ido da suke yi don a samar da wadataccen abincin.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatocin Jihohi da sauran abokan hadaka da su zuba kudade domin a wanzar da tsarin na kasa da a za a gudanar a watan Okotobar 2025, inda ya yi nuni da cewa, ba tare da an samar da bayanai da samar da kyakyanwan shiri zai yi wuya, a cimma burin da aka sanya a gaba.

A ra’ayin wannan jaridar, mun yi amannar cewa, kalubalen karancin abinci abu ne da ke bukatar hada karfi da karfe, wanda hakan zai wuce batun siyasantar da maganar da shelanta samar da Rumbunan adana hatsi.

Ya zama wajibi Gwamnatin Tarayya ta ayyana dokar ta baci wajen samar da wadataccen abinci tare da kafa tawaga mai karfi da za ta hada da Ma’aikatun Gwamnati, Hukumomin Tsaro, kungiyoyin Jin kai, Kamfanonin Masu Zaman Kansu da sauran masu ruwa da tsaki, musamman domin a samar da tare da kaddamar da kyakyawan tsari na kasa.

Dole ne Gwamnatocin Jihohi su marawa kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi kan zuba nannun jari wajen samar da abinci, samar da kayan adana amfanin gona, tsarin rabar da amafnin gonar, kuma kamfanoni masu zaman kansu, musamman masu yin noma domin samun riba, suma suna da gudunmawr da za su bayar wajen kara bunkasa fannin aikin noma, musamman domina a tabbatar da cewa, abincin ya isa ga teburin, musamman marasa karfi, wadanda kuma za su rinka sayen abincin, a cikin farashi mai sauki.

Ya zama wajbi UNICEF, FAO, WEF, da sauran takwarororin su, da su kara kaimi wajen aikin sa kai a yankunan da karancin abinci ya fi kamari, domin taimakawa Gwamnati wajen wanzar da aikin na dogon zango.

A zaman mu na kasa, ba ta sabu mu yi ikirarin cewa, kasar na kan turba ba, bayan alhali, ‘yan kasar na ci gaba da fuskantar yunwa.

 

Abinci
Ra'ayinmu
+ postsBio
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Next Post
2027: Tsananin Yunwa Zai Hana ‘Yan Nijeriya Sake Zaɓen Jam’iyyar APC – PDP

2027: Tsananin Yunwa Zai Hana ‘Yan Nijeriya Sake Zaɓen Jam’iyyar APC – PDP

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.