Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a taron manema labaru da aka saba yi a yau Litinin cewa, kamata ya yi kasar Amurka ta yi musayar bayanai da kididdiga game da annobar COVID-19 a fili, kuma kan lokaci tare da hukumar lafiya ta duniya (WHO), da ma sauran kasashen duniya.
Wasu rahotanni na cewa, a halin yanzu, cutar COVID-19 nau’in XBB.1.5 tana kara maye gurbin nau’in BQ.1.1, a matsayin nau’i na farko cikin sauri a Amurka. Game da hakan, Wang ya bayyana cewa, bayanai sun nuna cewa, a cikin shekaru uku bayan barkewar cutar, an samu yaduwar kusan dukkan nau’ikan cutar COVID-19 da rassanta a Amurka, wanda hakan ya sa ta zama daya daga cikin kasashen dake da nau’ikan cutar mafi yawa a duniya. Don haka, ya kamata Amurka ta yi musayar bayanai kan yanayin annobar da take ciki, tare da hukumar WHO, da sauran kasashen duniya kan lokaci, tare kuma da daukar kwararan matakai don hana ci gaban yaduwar cutar.
An kuma bayyana cewa, ma’aikatun harkokin wajen kasashen Jamus, da Belgium, da Luxembourg da dai sauransu, na ba wa ‘yan kasarsu shawarar kauracewa zuwa kasar Sin sai dai idan ya zama dole. Game da wannan batu, Wang ya ce, kasar Sin na fatan dukkan bangarorin za su kiyaye ka’idojin kimiyya, don tabbatar da zirga-zirgar mutanen daga kasashe daban-daban yadda ya kamata, da kuma ba da gudummawa ga hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar, da farfado da tattalin arzikin duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)