Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar fahimtar juna da ma’aikatar aikin hajji ta kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2023.
A ranar Talatar ne aka rattaba yarjejeniyar fahimtar junar da aka dade ana tsammnani a babban dakin taro na Super Dome da ke Jeddah na kasar Saudiyya.
Karamin Ministan Harkokin Waje, Amb. Zubair Dada ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatin Nijeriya, a wurin rattaba hannun akwai shugaban hukumar hajji ta Nijeriya ta kasa (NAHCON), Alhaji Zikrullah Kunle Hassan da kwamishinonin zartarwa uku na hukumar Nura Hassan Yakassai da Abdullahi Magaji Hardawa da Sheikh Suleman Mommoh da kuma shugabannin hukumar.
Daga cikin manyan batun da ke cikin yarjejeniyar shi ne tabbatar da guraben aikin Hajji 95,000 ga Nijeriya a bana, kujeru 75,000 ga Hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja da hukumomin tsaro ta Sojoji sai kuma sauran kujeru 20,000 da aka ware wa maniyyata masu zaman kansu (jirgin ‘yan kasuwa)