• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Taimakawa Yammacin Afrika Da Yankin Sahel

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Dai Bing, ya ce yankin yammancin Afrika da yankin Sahel, sun cimma muhimman nasarori wajen tabbatar da tsaro da farfado da harkokin raya tattalin arziki da zaman takewa da karfafa hadin gwiwa da goyon bayan juna, yayin da ake fuskantar yanayi mai tsanani a yankin da ma duniya baki daya.

Dai Bing ya bayyana hakan ne a jiya. Yana mai cewa, kasar Sin na mara baya ga kasashen yankin wajen karfafa tsarinsu na tsaro da zurfafa tuntubar juna da hadin gwiwa kan batutuwan tsaro da karfafa kafa dakarun yaki da ta’addanci na hadin gwiwa da sauran dabarun tsaro da kuma kokarin inganta karfinsu na tabbatar da zaman lafiya da yaki da ta’addanci.

  • Ina Fatan Na Kammala Mulki Lafiya Na Koma Katsina – Buhari

Ya kara da cewa, ya kamata kasa da kasa, musammam daddadun abokan hulda, su ci gaba da taimakawa tsaron yankin da samar da karin gudunmawa ga kasashen Sahel da suka hada da Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Niger, da ma sauran kasashen dake gaba-gaba wajen fama da matsalar tsaro, a fannonin samar da kudi da kayayyakin aiki da bayanan sirri da tsarin jigilar kayayyaki, domin karfafa karfinsu na yaki da ta’addanci.

Wakilin na Sin ya kuma nemi a mara baya ga tuntubar juna a harkokin siyasa da tattaunawa domin tabbatar da dorewar yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Ya ce a bana, an shirya gudanar da zabuka a wasu kasashen yankin, don haka, Sin na fatan ’yan siyasa a kasashen za su karfafa tattaunawa da cimma daidaito da samun ci gaba a harkokin siyasa domin bada kyakkyawar gudunmawa ga ci gaban kasashensu.

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

Bugu da kari, ya ce a matsayinta na ’yar uwa ga kasashen Afrika, kasar Sin za ta ci gaba da ba kasashen yammacin Afrika da yankin Sahel cikakken goyon baya, kuma ta shirya bayar da gudunmawa ga tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da kwanciyar hankali da ci gaban yankin. (Faeza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
Next Post
Masarautar Zazzau Ta Kori Wani Dogari Bisa Aikata Badala

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.