Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta sanarwar ta kara wa’adin mako daya don wadanda ba su karbi katin zabe su ba, su samu damar karbar ba.
Tun a farko dai, INEC ta kebe ranar 22 ga watan Janairu 2023 don kammala karbar katin na jefa kuri’a, ganin cewa, ta faro gudanar da aikin ne a ranar 12 ga watan Disamba, 2022.
- Shugaban Gabon Ya Gana Da Ministan Wajen Sin Kan Karfafa Alaka Tsakanin Kasashen Biyu
- Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Sadarwa
Sai dai, bayan wata tattauna wa da INEC ta gudanar a Abuja, ta yanke shawarar kara sabuwar ranar domin wadanda ba su karbi katin ba su samu damar karba.
Kwamishin ilimantar da masu jefa kuri’a na hukumar, Festus Okoye ne ya bayyana sabuwar ranar a cikin sanarwar da ya fitar.
Okoye ya ce, a bisa wannan sabuwar sanarwar, za a kammala karbar katin ne a ranar 29 ga watan Janairu 2023.
Ya ci gaba da cewa, bayan INEC ta shafe mako daya tana rabar da katin a ofis-ofis na kananan hukomomi ta kuma mayar da rabarwar da katin a cibiyoyin da aka yi rijista da kuma mazabu a ranar 6 ga watan janairun 2023.
Kwamishin ya kara da cewa, rabar da kati a mazabun a farko an tsara za a kammala a ranar 15 ga watan janairun 2023, amma bisa wannan sabuwar sanarwar, za a kammala karbar ne a ranar 22 ga watan Janairu 2023, inda ya kara da cewa, a ofis din kananan hukomomi kuwa, za a kammala karbar ne a ranar 29 ga watan Janairu 2023.