Gwamnatin Jihar Yobe, bisa jagorancin Hon. Mai Mala Buni ta sanya wa sabuwar kasuwar da ta kammala ginawa a garin Nguru a jihar (Nguru International Modern Market), sunan Shehun Malamin addinin musuluncin nan Shehu Muhammad Gibirima.
A sanarwar manema labaru, mai dauke da sa-hannun Darakta-Janar kan hulda da ‘yan jaridu da kafafen yada labarai a ofishin Gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed, da yammacin ranar Alhamis, Gwamnan ya sanar da hakan ne a lokacin da ya karbi bakoncin Malama Aisha AbdulMutalib, ‘yar asalin garin Potiskum, wadda da ta yi nasarar zama gwarzuwa a gasar karatun Alkur’anin Mai Tsarki (rukunin mata) a garin Gusau ta jihar Zamfara.
Gwamna Buni ya bayyana cewa ya sanya wa kasuwar sunan Shehin Malamin ne domin tunawa da gagarumar gudummawar da ya bayar wajen yada addinin musulunci a wannan nahiyar.
“Sannan kuma a matsayin sa na Malamin Addinin musulunci a fadin duniya, wanda al’ummar musulmin duniya ke girmamawa, bisa gudumawar da ya bayar.” In ji Buni.
Dangane da gwarzuwar gasar Alkur’anin kuwa, Gwamna Buni ya bayyana jindadinsa dangane da kokarin Malama Aisha, inda ya nunata a matsayin abin alfahari ga jihar Yobe.
Sakamakon haka, Gwamna Buni ya gwangwaje Hafiza Aisha da kyautar gida, kuma ya nadata a matsayin mai bashi shawara kan harkokin abubuwan da suka shafi haddar Alqura’ni Mai Tsarki, tallafin gurbin karatu da kujerar aikin Hajji tare da mijinta.
Har ila yau kuma, Gwamnan ya bai wa dukan yan kwamitin da suka jagoranci gasar karatun Alkur’anin zuwa samun wannan nasarar kyautar kujerun aikin Hajjin bana.
Alhaji Mamman Mohammed ya kara da cewa, Gwamna Buni ya jaddada ribanya kokarin gwamnatinsa wajen samar da ingantaccen ilimin addinin musulunci da na boko a jihar.
Gwamna Buni ya kara da cewa, kuma a matsayin jihar Yobe a cikin tsohuwar Daular Ngazargamo wadda aka santa da hidima tare da yada ilimin addinin musulunci, wannan zai ci gaba da kasancewa a zahiri wajen tanadar kyakkyawan sunan da aka san Daular da shi.