Shugabar kungiyar likitocin fisiyo da cututtukan koda (NAN), Dakta Adanze O Asinobi ta bayyana cewa a yanzu haka a Nijeriya akwai kimanin mutum miliyan 20 da ke fuskantar hatsarin kamuwa da cutar koda.
Shugabar NAN ta bayyana hakan ne a wurin taron kungiyar karo na 35 wanda ya gudana a Jihar Kano karkashin shugabancin kwamishinan lafiya, Dakta Ibrahim Aminu Tsanyawa, wanda aka yi a ranar Asabar da ta gabata.
- Gina Al‘ummar Sin Da Afirka Mai Koshin Lafiya Ba Batu Ne Na Fatar Baki BaÂ
- Me Sin Ta Kawo wa Duniya Cikin Shekaru 3 Da Ta Shafe Tana Kokarin Tinkarar Cutar COVID-19
Ta ce binciken da aka yi an gano cewa kashi 20 na al’umar Nijeriya na cikin barazanar kamuwa da cutar koda, kuma kashi 35 cikin 100 na kwanta dama a sanadiyar wannan cuta ta koda, domin haka akwai bukatar al’uma da hukumomi su dauki matakan kawar da cutar.
Shi ma shugaban kungiyar reshan Jihar Kano, Farfesa Aliyu Abdul ya ce akwai bukatar mutanen birni da na karkara da su yi kafa-kafa da shan magunguna na zamani da na gargajiya ba bisa umarnin likita ba ko kwararan masani, domin akwai cututtuka musamman na ciwon jiki da ke barazana wajen haifar da cutar koda, musammam wadanda ke da larurar cutar sikari da hawan jini da sauransu.
Tun da farko a jawabunsa, kwamishanan lafiya na Jihar kano, Dakta Ibrahim Aminu Tsanyawa, ya ce ganin wannan cuta ne ya sa gwamnatin Kano karkashin shugabancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta dau matakai na samar da kayayyakin aiki a asibitocin gwamnati, domin taimakawa da samar da lafiya ga masu wannan larura ta koda da sauran cututtuka da ke addabar mutane, musammam a manyan asibitocin mallakar Jihar Kano.