Wani masanin dangantakar Sin da Afrika a kasar Rwanda, Gerald Mbanda, ya ce ci gaban da kasar Sin ta samu ta hanyar kyakkyawan shiri da tunani da dabarun shugabanci na gari, abun karfafa gwiwa ne ga nahiyar Afrika, yayin da take kokarin raya tattalin arziki da inganta rayuwar jama’arta.
Gerald Mbanda, mai bincike, kuma mawallafi kan harkokin Sin da Afrika ne ya bayyana haka a baya-bayan nan, yayin da yake jawabi ga wani taro da aka yi a Kigalin Rwanda, kan tasirin babban taron wakilan JKS karo na 20 kan Rwandar.
A cewarsa, ci gaban Afrika zai kasance kan turbar da ta dace idan ta yi koyi da yadda kasar Sin ta yi, kuma take ci gaba da yi. Yana mai cewa, Sin da Afrika, sun kama hanyar samu wata makoma ta bai daya. (Fa’iza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp