Gwamnatin Nijeriya da sauran wasu kasashen duniya na tabka asarar sama da Dala Biliyan biyar a duk shekara sakamakon gurbatacciayar iska.
Babban Sakatare a ma’aikatar fasaha da kimiyya, Monilola Udo, ne ya sanar da hakan a Abuja a wani taron bita kan bunkasa kafar sadarwa ta yanar gizo don sa ido kan ingancin yanayi.
Monilola, ta ce bankin duniya ya danganta wannan asarar saboda rashin sa ido yadda ya dace.
Ta ci gaba da cewa, kafar yanar gizon na da mahimmanci matuka wajen sa ido kan ingancin yanayi da sa ido kan ingancin iska da ingancin ruwa.
A na sa jawabin tun da farko, Daraktan kula da muhallin kimiyya da fasaha a ma’aikar, Peter Ekwuozor, ya bayyana cewa, tsarin na kafar ta yanar gizo zai taimaka wajen kara ingancin tsarin da kuma dakile fitar da dagwalo daga masana’antun kasar da ke shafar kiwon lafiyar jama’a.