Jami’an hukumar ‘Yan sanda ta Akwa Ibom ta cafke fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finai ta Kudancin Nijeriya ‘Nollywood’, Moses Armstrong, kan zargin yi wa karamar yarinya ‘yar shekara 16 fyade.
Moses Armstrong, tsohon mai taimaka wa gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel a bangaren harkokin noma, ya na tsare ne a sashin kula da manyan laifuka (CID) da ke shalkwatar ‘yan sandan a Ikot Akpanabia.
- Nijeriya Da Wasu Kasashe Na Asarar Dala Tiriliyan 5 Duk Shekara Saboda Gurbacewar Iska
- ‘Yan Sanda Sun Ceto Matar Shugaban APC Na Jihar Neja Da Aka Sace A Borno
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa, ofishin matar gwamnan Jihar Akwa Ibom ne ya tsaya kai da fata sai an bi sawun lamarin a karkashin shirinta na taimakon iyali na ‘Family Empowerment and Youth Re-Orientation Path Initiative’ ( FEYReP).
Wani ma’aikacin ofishin matar gwamnan da ya nemi a sakaye sunansa ya shaida ma wakilinmu cewa, “Matar gwamnan ta na da ra’ayi sosai kan wannan kes din domin ganin an yi adalci kan yarinyar da aka keta wa haddi duk kuwa da cewa wanda ake zargin yana aiki a karkashin mijinta a matsayin daya daga cikin hadimansa.
“Ita matar gwamna ta damu sosai kan wannan lamarin, lura da cewa kes ne na fyade kuma kan karamar yarinya, ba ma kawai fyade ga karamar yarinya ba, ta tsani fyade da sauran klamuran da suka shafi cin zarafin mata a cikin al’uma.
“Don haka a shirye ofishinta ya ke ya bi sawun kes din nan tun daga farko har karshen shari’ar da za a tafka domin hukunta mai laifi da tabbatar da adalci.
“Yanzu haka muna jiran ‘yan sanda ne kawai su kammala gudanar da bincikensu,” a cewar jami’in.
Kazalika, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Supol Odiko Macdon, ya tabbatar da cafke jarumin, “Eh tabbas shi (Armstrong) yana tsare a karkashin kulawarmu, amma a bisa alamu yarinyar da ake magana a kai tana kokarin kaishi kasa ne saboda sun kasance abokai na wasu shekaru.”
A cewarsa Kakakin ‘yan sandan nan kusa kadan za su sake Wanda ake zargin bisa sharadin beli.