Dan takarar gwaman jihar Kaduna a jam’iyyar APC Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa, za a iya samar da ci gaba a cikin al’umma ne kawai idan akwai dawammamen zaman lafiya.
Sanata Uba Sani ya yi wannan bayani nea yayin ganawa da al’ummar Manchok, shalkwar karamar hukumar Kaura, inda ya yi alkawarin kirkiro da sana’o’in hannu, musamman ga mata da matasa don su zama masu dogaro da kan su ganin cewa gwamnati ba za ta iya daukar dubban matasan da ke a jihar ba aiki ba.
“Ilimin boko na da matukar mahimmanci wurin kara inganta rayuwar ko wacce irin al’umma tare da kuma habaka tattalin arzikin al’ummar.” In ji shi.
Dan takarar ya kara da cewa, akwai gibin da ake da shi na koyon sana’o’in hannu a jihar Kaduna wanda akwai matukar bukatar a cike shi.
A cewar sa, Idan al’ummar jihar Kaduna su ka kada masa kuri’un su a shekarar 2023, gwamnatin sa za ta tabbatar da bayar da horo ga matasa a fannin koyon sana’o’in hannu domin su kasance sun tsaya da kafafun su, musamman domin a kara ciyar da tattalin arzikin jihar a gaba.
Sai dai kuma, Sanata Uba Sani ya ce, “Za a iya samun wannan nasarar ce, idan akwai dawammamen zaman lafiya. Ya zama wajibi mu mayar da hankulan mu wurinn ciyar da jihar da kuma Nijeriya gaba.
Sanatan ya yi nuni da cewa, dole ne mu tabbatar da mun kau da dukkan banbance -banbance na kabila da na addini domin samun kai wa ga gaci.
Dan takarar kafin gudanar ganawar sa da gangamin yakin neman zaben sa a garin, ya kuma kai zirar ban girma ga Cif na Atakar.
Daga bisani, Sanata Uba Sani ya kuma ziyarci Kafanchan shalkwar karamar hukumar Jema’a, Kaura da Zangon Kataf, inda ya yi wa al’umma jawabi tare da yin kira a gare su da su zabi jam’iyyar APC tun daga kasa har sama a zaben shekarar 2023.