Majalisar Dinkin Duniya (UN) da Kungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) sun gargadi Nijeriya game da rikicin zaben 2023.
Yayin da UN ta yi gargadin cewa, idan har abubuwa suka ci gaba da tabarbarewa a Nijeriya, to za a samu mummunan sakamako ga zaman lafiya da kwamciyar hankali a kasar baki daya, sannan kungiyar ECOWAS ta ce idan aka samu tashin hankali a Nijeriya, babu wata kasa a yankin Yammacin Afirka da za ta iya daukar ‘yan gudun hijirar Nijeriya.
- Yadda Ake Kafa Kamfanin Burodi
- An Watsa Shirin Bidiyo Na Tallata Shagalin Murnar Bikin Bazara A Wurare Daban Daban Na Duniya
Sun dai yi wannan gargadin ne a garin Jos, Babban Birnin Jihar Filato a wurin wani taro na bayar da horon sasantawa da hulda da hadakan kungiyoyin da sauran masu ruwa da tsaki wadanda suka fito daga yankin arewa ta tsakiya da arewa maso gabas kan dakile rikice-rikicen zaben 2023.
An bayar da rahoton cewa sama da mutum 30 ne suka rasa rayukansu, sannan da dama sun jikkata sakamakon rikice-rikicen zaben 2023 a wasu sassan Nijeriya.
Haka kuma an sa sha kai hare-hare a ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), musamman a yankin kudu maso gabashin Nijeriya, wadanda yawancinsu suna da alaka da haramtacciyar kungiyar nan mai fafatukar kafa kasar Biafara (IPOB), lamarin da ya kai ga kashe ma’aikatan INEC da jami’an tsaro da dama.
Da take jawabi a wurin taron, wakiliyar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yammacin Afirka, Sa’adatu Sha’abu ta ce, “Idan har al’amura suka ci gaba da yin tsami a Nijeriya, za a samu mummunan sakamako ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan yankin yammacin Afirka.”
Jami’in tsare-tsare na kungiyar ECOWAS, wanda ya kasance mai shiga tsakani Brown Odigie ya ja kunnen masu ruwa da tsaki kan gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali da lumana.
Odigie ya kasance wakilin kwamishinan kungiyar ECOWAS kan harkokin siyasa, zaman lafiya da kuma tsaro, Abel Fatau ya bukaci dukkan ‘yan takara da jam’iyyunsu da su martaba yarjejeniyar zaman lafiya da suka sanya wa hannu da kuma ka’idojin zaben 2023.
Ya ce, “Wannan wani sasanci ne da ake yawan yi a kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS. Muna yin wannan lamari a Nijeriya ne, saboda Nijeriya ta kasance babbar mamba a kungiyar ECOWAS.
“Nijeriya na da dimbin al’umma. Zaben na iya haifar da rikici idan har ba a gudanar da shi yadda ya kamata ba. Kuma idan har aka samu rikici, zai iya shafar sauran kasashe makwabta saboda dinbin jama’an da Nijeriya take da su. Ina mai tabbatar muku da cewa babu wata kasa a cikin kungiyar ECOWAS da ke da karfin daukar ‘yan gudun hijira daga Nijeriya.”
Sakataren gamayyar kungiyoyin na kasa, Yusuf Dantalle ya bayyana cewa ‘yan saiyasa sukan shiga halin kaka-ni-ka-yi a lokacin da suka yi rashin nasara, saboda makudan kudaden da suke kashewa a zabe.