Jiya Asabar shi ne jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta al’ummar kasar Sin, wato shekarar zomo, inda babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar, ko kuma CMG a takaice, ya gabatar da wani gagarumin shagalin murnar ranar, dake kunshe da wasanni masu burgewa, da sabbin fasahohi masu ci gaba, da kade-kade da raye-raye masu jawo hankali.
Ya zuwa karfe 2 na asubahin yau Lahadi 22 ga wata, gaba dayan masu kallon shagalin ta hanyoyi daban-daban ya zarce biliyan 11, ciki har da kaso 50.51 bisa dari na mutane masu shekaru 15 zuwa 44 da haihuwa, kuma yawan mutanen da suka kalli shagalin kai-tsaye ta hanyar sadarwar intanet, da kuma yawan mutanen da suka kalli shagalin a kasashen ketare, duk sun kai matsayin koli a tarihi. (Murtala Zhang)