Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Nijeriya (NRC), ta nemi afuwar jinkirin da aka samu yayin zirga-zirgar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin.
Pascal Nnorli, Manaja, Hukumar Jiragen kasa ta Abuja-Kaduna (AKTS) ne, ya fitar da sanarwa bayan korafin da fasinjojin suka yi.
- Allah Ya Yi Wa Jarumin Kannywood, Abdulwahab Awarwasa Rasuwa
- Diphtheria: Mutane 123 Sun Kamu, 38 Sun Mutu A Jihohi 4 – NCDC
Nnorli ya bayyana cewa an samu tsaikon ne saboda karancin man dizal.
Ya ce man dizal din ya gaza ma’aunin da ake bukata kuma babu yadda za a yi jirgin ya tashi ba tare da isasshen mai ba.
Manajan ya ce ana tabbatar da cewar kowane jirgi na da isasshen mai bayan gwaji da ake masa kafin tashi.
Sanarwar ta ba da tabbacin cewa ayyukan za su daidaita yayin da ake sa ran komai ya kan-kama.
An dawo da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 5 ga Disamba, 2022, bayan shafe sama da watanni takwas bayan harin ta’addanci da kai wa jirgin a watan Maris din 2022.
Kimanin mutane 14 ne aka kashe sannan aka sace akalla 63 a ranar 28 ga Maris, 2022, a Katari da ke Jihar Kaduna.
An sako rukunin karshe na mutane 23 da aka sace a watan Oktoba bayan sakin mutane bakwai a watan Yulin 2022.