Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da wani hatsarin mota ya rutsa da rayukan wasu fadawan Shehun Borno guda uku, Alhaji Abubakar Umar Ibn Garbai El-kenmi, a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
Kwamandan Hukumar a Jihar Borno, Utten Iki Boyi, ya shaida hakan a Maiduguri da safiyar ranar Talata cewa mutane shida ne suka yi hatsarin wanda ya auku a ranar Litinin, amma an ceto uku, inda aka kai su wani asibiti da ke kusa.
- Yadda Karancin Mai Ya Hana Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Tashi
- Makamashi Mai Tsafta Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Isasshen Makamashi A Sin
A cewarsa, lamarin ya faru ne a kusa da yankin Benisheik lokacin da motar ta yi dungure sannan ta kama da wuta.
Ya ce nan da nan suka tura jami’an su zuwa wajen da lamarin ya faru, inda aka samu mutum uku sun kone kurmus kuma har ba a iya gane su.
Sai dai ya ce an samu nasarar ceto mutum uku inda aka kai su zuwa babban asibitin Beneshiek don yi musu magani.