Hukumar kidaya ta kasa ta fara horar da ma’aikata 786,741 domin kidayar jama’a a 2023.
Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar, Isiaka Yahaya, ya fitar ta yi karin haske kan horar da ma’aikatan.
- Fadawan Shehun Borno 3 Sun Kone A Hatsarin Mota
- An Nuna Shagalin Murnar Shiga Sabuwar Shekarar Gargajiyar Kasar Sin Da CMG Ya Tsara A Afirka
Akwai masu aiki kididdige mutane 623,797, masu kula da aikin 125,944, mataimakan inganta bayanai 24,001, da masu gudanar da tsare-tsare 12,000.
Sauran su ne manajoji 1,000, masu tafiyar da al’amuran cibiyoyi 1,639, da masu gudanarwa a matakin matakin kananan hukumomi 59,000.
An tsara horon ne ga dukkan jihohi da kuma babban birnin tarayya Abuja.
An fara horar da ma’aikata na musamman da masu gudanarwa na kidayar jama’a a ranar Litinin.
Ya ce horon ya kunshi nazarin koyon horo na kai da kai, sai kuma horo na kai tsaye da za a ba su da kuma horo kan yadda za a amfani da fasahar sadarwa ta Intanet.
Za a koyar da ma’aikatan kan yadda za su dauki bayanan mutane a fom din kidayar, hanyoyin daukar bayanai, sadarwar jama’a, da warware matsalar komfuta.
NPC ta kuma dauki aiki tare da horar da manajojin da za su inganta bayanai da mataimaka na musamman don gudanar da aikin.
Za a fara gudanar da kidayar yawan jama’a da gidaje ta 2023 daga ranar 29 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu.