Da karfe 3:49 na safiyar yau Alhamis 26 ga watan nan, girgizar kasa mai karfin maki 5.6 ta afku a gundumar Luding dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin.
Bayan abkuwar girgizar kasan, nan da nan sashen kula da harkokin gaggawa na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya ba da jagoranci kan aikin ceto da na binciken halin bala’in. Ya zuwa yanzu, an riga an kammala aikin ceton gaggawa, kuma babu hasarar rayuka, ko rugujewar gidaje a yankin da bala’in ya afku, kana hanyoyi, wutar lantarki, sadarwa, da tsarin samar da ruwan sha, duk sun dawo yadda ya kamata. (Mai fassara: Bilkisu Xin)