Idan Allah ya kaimu ranar Talata 31 ga watan Janairun 2023, Kamfanin LEADER-SHIP zai gudanar da babban taronsa wanda ya saba gudanarwa a duk shekara.
Taron karo na 14 da zai gudana a Babbar Cbiyar Taro ta Duniya da ke Abuja.
- A Sake Lale Kan Mayar Da Tubabbun ‘Yan Boko Haram Jihohinsu Na Asali
- Majalisa Ta Tabbatar Da Arase A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Kula Da ‘Yansanda
Ana sa ran Tsohon Firaministan Kenya, Raila Amolo Odinga zai kasance babban bako mai jawabi inda zai gabatar da makala mai taken “sahihin zabe da tattalin arziki a yanayin sauyi”.
Har ila yau, mai martaba Etsu Nupe kuma shugaban majalisar sarakunan Jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar shi ne zai kasance uban taro a ranar.
Wasu manyan masu rike da mukamai za su raka sarkin zuwa dakin taron na LEADERSHIP da kuma bayar da lambar yabo.
Babban taron na LEADERSHIP dai, zai kuma kunshi gabatar da lambobin yabo ga wasu fitattun ‘yan Nijeriya da kungiyoyi da suka nuna bajinta wajen kawo ci ga-ban kasa da na al’umma daban-daban.
Idan dai ba a manta ba, Kamfanin LEADERSHIP ya sanar da karrama wasu masha-huran mutane a shekarar 2021, wadanda suka hada da shugaban Bankin Afredim, Farfesa Benedict Oramah da shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, (NDLEA) Birgediya Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) da kuma Olu-watobilobi Ayomide Amusan, wadanda suka lashe kyautar zama gwarazan kam-fanin a shekarar 2021.
A taron na bana, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru el-Rufa’I yana daya daga cikin gwarazan gwamnoni wanda zai samu karramawa bisa kyakkyawan shugabancinsa, musamman kokarin da ya yi na kawo canji a Jihar Kaduna ta han-yar bunkasa tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da ba a taba ganin irinsa ba da kuma gyara ma’aikatun gwamnati da cibiyoyin hukuma a jihar.
Haka shi ma Gwamna Abiodun ya samu nasarar lashe kyautar zama gwarzon gwamnan na shekara, saboda himmarsa wajen samar da ababen more rayuwa da kuma ci gaban da ya samu na fadada martabar kasuwanci a jiharsa.
Shi ma Gwamna Ifeayi Ugwanyi ya lashe lambar yabo ta gwarzon gwamnan she-karar 2022, saboda dora jiharsa kan turbar samun ‘yancin gashin kai da kuma samar da ci gaba a bangaren ababen more rayuwa a fadin jiharsa, duk da kalu-balen tsaro da jihar ke fuskanta.
Wadanda suka kasance gwarazan shugabannin ma’aikatun gwamnati da kamfan-in LEADERSHIP zai karrama sun hada da shugaban hukumar tara haraji ta kasa (FIRS), Muhammad Mamman Nami da Darakta Janar na Asusun Horaswa na (ITF), Joseph Ari, da kuma Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Isa Jere Idris.
Bankin LOTUS shi ne ya lashe gwarzon bankin shekara na LEADERSHIP, saboda sabbin abubuwan da ya kawo na kare martabar masu hannun jari.
Har ila yau, za a karrama, Fasto Solomon Folorunsho a matsayin gwarzon kyau-tata rayuwar al’umma, saboda irin gudummar da gidauniyarsa ta bai wa jama’a duk da karancin kudaden da ake fuskanta.
A bangaren gwarzuwar shugaban banki kuma, Manajan Daraktan Bankin Fidelity, Misis Nneke Onyealu-Ikpe, ce ta lashe bisa jajircewarta wajen tallafa wa kananun ‘yan kasuwa da kudade a rassa daban-daban. Yayin da Manajan Daraktan Mojec International Holding, Misis Chantelle Abdul ta kasance gwarzuwar ‘yar kasuwa ta shekara.
Hukumar NSCDC ita ce ta lashe kyautar gwarzuwar hukumar gwamnati ta she-karar 2022, bisa gagarumin ci gaba da hukumar ta samu a cikin shekara daya.
Sauran wadanda za a karrama sun hada da gwarzon kamfanin shekara wanda za a bai wa BUA, bisa zama kamfanin da ke da mafi kyawon hannun jari a wannan shekarar, yayin da MTN kuma ya lashe gwarzon kamfanin sadarwa na shekara bisa kwarewarsa wajen sadarwa.
Mama Pride, daya daga cikin shinkafar gida wanda ta yi saurin karbuwa ita ce ta lashe gwarzuwar kayan kamfani na shekara.
Bugu da kari, Kamfanin LEADERSHIP zai bayar da kyautar gwarzon sashen mai da gas da ke amfani da kayan cikin gida ga Babban Sakataren hukumar kula da ci ga-ban abububuwan da ake samarwa a Nijeriya, Mista Simbi Wabote.
A wannan shekarar, mawakin nan mai wakar Turanci na bangaren kade-kade da wake-waken Afro Pop RnB-hop, Kiss Daniel shi ne ya lashe gwarzon dan nishadi.
Tawagar ‘yan kwallo mata na ‘yan kasa da shekaru 17 ta Nijeriya ita ce ta lashe lambar yabon gwarzuwar tawagar ‘yan wasa, bisa yadda ta wakilci kasar a gasar FIFA, inda ta ci wa Nijeriya lambar yabo a gasar Olympic ta lokacin zafi da aka gudanar a Rio de Janeiro ta kasar, yayin da wani yaro dan shekara 13 dan aji hudu a matakin firamare mai hazaka daga Jihar Borno, Musa Sani, wanda ya zana fa-salin gadar sama ta Maiduguri ta hanyar amfani da laka, ya lashe kyautar LEAD-ERSHI ta gwarzon matashi na shekara.
Za a fara gudanar da babban taron ne dai da hantsin ranar Talata zuwa azuhur.